Tinubu ba Ya Sauraron Kokenmu, Gwamnan Bauchi Ya Nemi Sheikh Jingir Ya Shiga Tsakani

Tinubu ba Ya Sauraron Kokenmu, Gwamnan Bauchi Ya Nemi Sheikh Jingir Ya Shiga Tsakani

  • Gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed, ya bayyana rashin jin dadinsa da salon mulkin Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu
  • Ya nuna damuwa kan gyaran dokar haraji da gwamnatin tarayya ta kawo, wanda zai iya kara jefa jihohi a cikin mawuyacin hali
  • Bala Mohammed ya bukaci Sheikh Sani Yahaya Jingir ya yi amfani da matsayinsa wajen isar da koken jama'a ga Tinubu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Bauchi - Gwamnan jihar Bauchi, Bala AbdulKadir Mohammed ya bayyana cewa ba sa goyon salon mulkin shugaba Bola Ahmed Tinubu.

Gwamnan ya fadi ra'ayinsa ne a lokacin da ya ke tattaunawa da fitaccen Malamin addinin Muslunci, Sheikh Sani Yahaya Jingir tare da muka bukatunsa.

Bauchi
Gwamnan Bauchi ya jaddada adawa da kudirin haraji Hoto: @SenBalaMohammed/@OfficialBAT
Asali: Twitter

A wani bidiyo da Hassan Ibrahim ya wallafa a shafinsa na Facebook, an gano yadda gwamna Bala Mohammed ya fadi matsalarsu da gwamnatin Bola Tinubu.

Kara karanta wannan

Dan Bilki Kwamanda: Abba ya hana ni zuwa aikin hajji duk da taimakon Kashim Shettima

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya shaida cewa ya ji dadin ganawa da Sheikh Jingir, ganin cewa zai iya fada wa shugaba Tinubu koken 'yan Najeriya, kuma a saurare shi.

"Matsalarmu da gwamnatin Tinubu," Gwamnan Bauchi

Gwamnan Bauchi, Bala Mohammed ya yi zargin cewa shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ba ya karbar shawarwari duk da koken 'yan kasa.

Kauran Bauchi ya kara da cewa ;

"Da gaske ne ba mu shiri da shi. Saboda 'yan uwanmu suna shan wahala, mu ma gwamnoni mu na shan wahala, sakamakon abubuwa, kudurori da ya kawo wanda ba ya sauraron mutane."
"Kuma ba ya ji, ba ya gani, abin kamar zai hallaka al'umar Arewa da al'umar Najeriya."

Gwamnan Bauchi ya soki kudirin haraji

Gwamnatin jihar Bauchi ta bayyana takaicin yadda Arewacin Najeriya ta dogara da kudin da gwamnatin tarayya ke raba wa jihohi, wanda ake samu daga albarkatun kasa.

Bala Mohammed ya ce wannan ce ta sa yankin ke kuka da kudirin gyaran dokar haraji da gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ta bijiro da shi, wanda aka ce ba za a janye ba.

Kara karanta wannan

Gwamnan da ke sukar kudirin gyaran haraji ya koma goyon bayan tsarin Tinubu

Ya ce;

"Idan aka tsuke aljihun kudin haraji ga jihohi irinmu, to za a wahala ninkin-ba-ninkin.

Gwamnan Bauchi ya mika bukata ga Jingir

Gwamnan PDP da ke jagorancin jihar Bauchi, Bala Mohammed ya mika sako ga daya daga cikin Malaman da suka yi wa'azin a zabi Muslim-Muslim a zaben 2023.

Gwamnan ya bayyana cewa kila Sheikh Sani Yahaya Jingir ya na daga cikin masu ba Shugaba Tinubu shawara a kan matsalolin da ya jefa Najeriya a matsala.

"Abubuwan da Shugaban kasa ya ke kudurawa, ba sa aiki. Kuma muna bukatar irinku dama da Allah Ya bamu a cikin al'umma, wanda kowa na sa ne kuma za su tursasa kowa.".

Gwamnan jihar Bauchi ya yi nade-nade

A wani labarin, mun ruwaito cewa gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed ya bayar da sababbin mukamai ga wasu daga cikin kwamishinoninsa da ya sallama daga aiki.

Kara karanta wannan

Rikici ya ƙara tsanani, an gano mai zuga gwamna ya yi wa Bola Tinubu 'rashin kunya'

Awanni kadan bayan ya yi wa gwamnatinsa garambawul, Gwamna Bala Mohammed ya nada uku daga cikin kwamishinonin da ya kora a matsayin masu ba da shawara.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.