'Ka Kawo Mana Ɗauki': An Faɗawa Tinubu Garuruwa 2 da Boko Haram Ta Ƙwace a Borno

'Ka Kawo Mana Ɗauki': An Faɗawa Tinubu Garuruwa 2 da Boko Haram Ta Ƙwace a Borno

  • Kakakin majalisar Borno ya bukaci gwamnatin tarayya ta kafa birgediyar soja a kananan hukumomin Guzamala da Kukawa
  • Rt. Hon. Abdulkarim Lawal ya koka kan cewa har yanzu garuruwan biyu na hannun Boko Haram duk da kiraye-kirayen da yi
  • Shugaban majalisar ya yaba wa Gwamna Babagana Zulum kan kokarin kawo ci gaba a jihar duk da kalubalen tsaro da ake fuskanta

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Borno - Shugaban majalisar Borno, Abdulkarim Lawan, ya bukaci gwamnatin tarayya ta kafa sansanin birgediyar soja a wasu kananan hukumomin jihar.

Rt. Hon. Abdulkarim Lawal ya ce akwai bukatar samar da birgediyar soja domin ’yantar da kananan hukumomin Guzamala da Kukawa daga Boko Haram.

Shugaban majalisar Borno ya yi magana kan garuruwan da Boko Haram suka kwace
Shugaban majalisar Borno ya nemi taimakon gwamnati kan garuruwan da Boko Haram ta kwace. Hoto: @GblModu18379, @NGRPresident
Asali: Twitter

An roki Tinubu ya kafa birgediyar soji a Borno

Rahoton Daily Trust ya nuna cewa birgediyar soja na kunshe da bataliya mai dauke da sojoji tsakanin 3,000 zuwa 5,000 tare da manyan kayan aiki.

Kara karanta wannan

Kotu ta saki Mubarak Bala, matashin da aka daure kan zargin batanci ga addini

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shugaban majalisar, wanda ke wakiltar Guzamala, ya yi wannan kiran ne yayin da yake jawabi ga manema labarai kan karin kasafin kudi da aka amince da shi.

Rt. Hon. Abdulkarin ya koka cewa fiye da shekaru goma kenan Boko Haram suka mamaye Guzamala da Kukawa duk da kiran da aka sha yi na kwato yankin.

Halin da ake ciki a wasu garuruwan Borno

Shugaban majalisar ya bayyana cewa babu farar hula ko na soja a Guzamala, sai wasu sojoji kadan da suke a garin Abadam.

"Farar hula ba su da ikon shiga Guzamala da Kukawa fiye da shekaru goma kenan. To, menene sojoji suke yi a wurin?
"Ina kira ga gwamnatin tarayya da sojojin Najeriya da su kafa rundunar sojar birgediya a Guzamala don dawo da tsaro."

- A cewar shugaban majalisar.

"Boko Haram sun sake kwace Mariri" - Shugaban majalisa

Ya jaddada muhimmancin kawo tsaro domin ’yan gudun hijira su koma gidajensu na asali.

Kara karanta wannan

Gwamnan da ke sukar kudirin gyaran haraji ya koma goyon bayan tsarin Tinubu

Rt. Hon. Abdulkarim ya ce:

"Ina matuƙar jin takaici idan ina ganin mutanena suna rayuwa a matsayin ’yan gudun hijira ko kuma bakin haure a kasashe makwabta."

Duk da haka, ya yaba wa Gwamna Babagana Zulum bisa kokarinsa wanda ya kai ga dawo da mutane zuwa kauyen Mairari tare da basu kayan tallafi.

Sai dai ya bayyana cewa ’yan ta’adda sun sake kwace Mairari saboda rashin kayan yaki da bindigogi da jami’an tsaro suka fuskanta.

Majalisa: "Dalilin kara N31bn a kasafin 2025"

Dangane da karin N31bn a kasafin kudi na 2025, Vanguard ta rahoto Rt. Hon. Abdulkarim Lawal ya ce an yi hakan ne da nufin cike gibin kasafin muhimman bangarori.

Ya jaddada cewa bangaren lafiya ya na fifiko, shi ya sa aka kara masa kudi domin kammala asibitin koyarwa da inganta ayyuka a cibiyoyin lafiya da aka kafa a 2024.

A game da ware Naira biliyan biyar ga ma’aikatar rage talauci da habaka matasa, ya ce hakan zai taimaka wajen rage radadin rashin tsaro a jihar.

Kara karanta wannan

Kudin hajji: Gwamna Abba ya nemawa Musulmai alfarma a wajen Tinubu

Zulum ya rattaba hannu kan kasafin 2025

An ji mun ruwaito cewa, a ranar Litinin, Gwamna Babagana Zulum ya rattaba hannu kan kasafin 2025 na N615.8bn, bayan karin N31.1bn da aka yi.

Tun farko, gwamnan ya gabatar da kasafin Naira biliyan 584.76 mai taken “Kasafin farfadowa da ci gaba,” kafin majalisar dokoki ta gyara ta kara kudin.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.