Yan Bindigar da Suka Halaka Sojoji Sun Gamu da Ajalinsu, An Harbe Su Har Lahira
- Dakarun sojoji sun kama miyagun ƴan bindigar da ake zargi da kashe sojoji huɗu a jihar Ribas da ke Kudu maso Kudancin Najeriya
- Rundunar soji ta shida da ke Fatakwal ta ce sojojin sun kashe ƴan ta'addan bayan sun yi yunkurin guduwa, an kwato mugayen makamai
- Kakakin rundunar, Laftanar Kanal Ɗanjuma Ɗanjuma ya ce sojoji ba za su runtsa ba a ƙoƙarinsu na tsare rayuka da dukiyoyin ƴan Najeriya
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Rivers - Rundunar sojin kasa ta Najeriya ta ce dakarunta sun yi nasarar kashe miyagun ƴan bindigar da ake zargi da kisan sojoji huɗu a jihar Ribas.
Mai magana da yawun rundunar soji ta 6 da ke sansani a Fatakwal, babban birnin Ribas, Danjuma Danjuma, ne ya bayyana haka cikin wata sanarwa a ranar Talata.
Dakarun sojojin sun hallaka ƴan ta'addan ne a jihar da ke Kudu maso Kudancin Najeriya, kamar yadda jaridar Premium Times ta ruwaito.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sojoji sun murƙushe ƴan bindiga a Ribas
Ɗanjuma Ya ce dakarun bataliya ta biyar sun kashe 'yan ta'adda biyu yayin wani samame da suka kai a Kalaogbokolo, ƙaramar hukumar Ahoada ta Yamma a Ribas.
Kakakin rundunar ya ce:
"Wannan ƙungiyar ƴan ta'addan ce ta kashe sojoji hudu tare da yin garkuwa da wasu injiniyoyi biyu 'yan asalin Koriya, waɗanda ke aiki da kamfanin Daewoo Nigeria Limited ranar 12 ga Disamba, 2023.
“A farko sojoji sun kama mutum biyu daga cikin ƴan ta'addan da suka kai samame amma daga bisani suka harbe su har lahira bayan sun yi yunkurin tserewa cikin daji.
"Dakarun sojin sun yi artabu da ƴan bindigar yayin da suka kai samamen kafin su murƙushe su,” in ji shi.
Laftanar Kanal Danjuma ya ce sojojin sun yi nasarar kama masu laifin ne bayan samun sahihan bayanan sirri da suka nuna cewa sun shigo cikin gari.
Sojoji sun kwato manyan makamai
Ya ce dakarun sojin sun kwato bindiga samfurin AK-47, samfurin Fabrique National, da kuma wata bindiga guda ɗaya, Leadership ta rahoto wannan.
Sauran kayan da aka ƙwato sun haɗa da bindigogin gida guda biyu, AK-47 Magazines guda uku, harsashi guda uku samfurin na musamman, da kuma harsasai guda 13 samfurin NATO.
Rundunar Sojojin Najeriya ta ƙara tabbatar da cewa, duk tsawon lokacin da za a ɗauka, masu hannu a kisan dakarun soji huɗu za su shiga hannu kuma doka za ta yi aiki a kansu.
Sojoji sun lashi takobin tsare ƴan Najeriya
Ta kuma ƙara bai wa ƴan Najeriya tabbacin cewa jami'an soji ba za su yi ƙasa a guiwa ba wajen kare rayuka da dukiyoyin al'umma.
Rundunar ta ƙara karfafa wa mutane guiwa da su ci gaba taimakon jami'an tsaro da sahihan bayanan sirri domin kakkabe ƴan ta'adda da dawo da zaman lafiya.
Wani jagoran ƴan bindiga ya baƙunci lahira
A wani labarin, kun ji cewa dakarun sojoji sun hallaka wani ƙasurgumin ɗan bindigar daji da ya hana mutane zamana lafiya a Tsafe, jihar Zamfara.
Ɗan ta'adda, Sani Rusau ya bakunci lahira a hannun sojoji yayin da suka kai samame maɓoyarsa bayan samun bayanan sirri.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng