'Ku Kori Kanku Kafin a Kore Ku': Malamin Musulunci ga na Kusa da Tinubu kan Bello Turji

'Ku Kori Kanku Kafin a Kore Ku': Malamin Musulunci ga na Kusa da Tinubu kan Bello Turji

  • Malamin addinin Musulunci, Sheikh Murtala Bello Asada ya caccaki gwamnatin Bola Tinubu kan ta'addancin Bello Turji
  • Malamin ya ce abin takaici ne yadda dan ta'addan ke cin karensa babu babbaka har umarni Bello Turji ke ba gwamanti saboda lalacewa
  • Sheikh Asada ya bukaci masu ba shugaban shawara musamman a bangaren tsaro su ajiye mukamansu kafin a kore su
  • Wannan na zuwa ne yayin da Turji ya yi gargadi idan ba a sake masa yan uwansa da aka kama ba za a fuskanci hare-hare a 2025

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Sokoto - Sheikh Murtala Bello Asada ya yi magana kan ta'addancin Bello Turji a yankin Arewacin Najeriya da yadda za a dakile matsalar.

Shehin malamin ya ce abin kunya ne yadda mukarraban wannan gwamnati ba su jin kunyan kallon fuskokin yan Najeriya duk da kuntata musu da ake yi.

Kara karanta wannan

'Na san za a zage ni': Tinubu ya fadi shirin da yake yi wa Najeriya

Malamin Musulunci ya caccaki hukumomi kan ta'addancin Bello Turji
Sheikh Murtala Bello Asada ya ce abin kunya ne abin da Bello Turji ke yi hankali kwance a Arewacin Najeriya. Hoto: Malam Murtala Bello Asada, Asiwaju Bola Tinubu.
Asali: Facebook

Turji: Sheikh Asada ya soki mukarraban Tinubu

Shehin malamin ya fadi haka ne a cikin wani faifan bidiyo da Abdullahin Gwandu TV ya wallafa a shafin Facebook.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sheikh Asada ya ce abin kunya ne a ce hukumomin Najeriya suna hada ido da yan Najeriya saboda yadda suka ci amanarsu musamman a bangaren tsaro.

Ya shawarci masu ba shugaban ƙasa shawara musamman ta bangaren tsaro da su ajiye aikinsu kafin ya kore su.

Sheikh Asada ya shawarci masu rike da mukamai

"Ya kamata masu jagorancin wannan kasa su ji kunyan hada idanu da mutane, a ce yau akwai dan ta'adda da ke ba gwamnati umarni, don Allah an ji kunya ko ba a ji ba?"
"Gwamnatin Najeriya idan suna da hankali da tunani duk wanda ke kan wata kujera ta tsaro idan aka yi wata daya ba a kama Bello Turji ba Wallahi ya kamata a kora shi."

Kara karanta wannan

Kudirin haraji: Malamin musulunci ya ba Arewa shawarar gujewa zaman gori

"Ya kamata shugaban sojoji da ministocin tsaro babba da karami da mai shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro, Malam Nuhu Ribadu su sauka idan aka yi wata daya ba a kama ko kashe Bello Turji ba."

- Sheikh Murtala Bello Asada

Sheikh Asada ya yi fatali da maganar sulhu

Sheikh Asada ya ce idan da irin haka na faruwa ne a wata ƙasa ta daban da mafi yawan masu mukamai musamman a bangaren tsaro sun ajiye aikinsu.

Malamin ya kuma soki masu cewa a yi sulhu inda ya ce irin yarjejeniya da ke yi da Bello Turji babu komai sai zaluntar yan Arewa.

Turji ya gargadi hukumomi kan cafke yan uwansa

Mun ba ku labarin cewa kasurgumin dan ta'adda, Bello Turji ya fitar da sabon bidiyo, yake gargadi ga hukumomi a jihar Sokoto kan cafke wasu yan uwansa.

Dan ta'addan ya bukaci a yi gaggawar sake musu yan uwansu da ke hannun hukumomi ko kuma su fuskanci sababbin hare-hare a cikin sabuwar shekarar 2025.

Kara karanta wannan

"Ba gwamnati ta jawo tsadar rayuwa ba," Malamin musulunci ya faɗawa ƴan Najeriya gaskiya

Wannan na zuwa ne bayan wasu rahotanni sun tabbatar cewa an cafke wasu daga cikin mataimakan Bello Turji da ake ganin zai iya yin komai a kansu domin ceto su.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.