Kaduna: Sanatan PDP Ya Yi Martani kan Shirin Yi Masa Kiranye daga Majalisa

Kaduna: Sanatan PDP Ya Yi Martani kan Shirin Yi Masa Kiranye daga Majalisa

  • Sanata Lawal Adamu Usman bai ji daɗin batun yi masa kiranye da ƙungiyar dattawan Kaduna (KEF), ta fara ba
  • Ɗan siyasar na jam'iyyar PDP ya bayyana cewa shirin yi masa kiranye da ƙungiyar ke yi ba komai ba ne face abin dariya
  • Sanatan ya zargi ƙungiyar da yin aiki domin cika burace-buracen wasu ƴan siyasa da suke fakewa da su domin yaƙarsa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Kaduna - Sanata mai wakiltar Kaduna ta Tsakiya, Lawal Adamu Usman, ya yi martani kan shirin yi masa kiranye da ƙungiyar dattawan Kaduna (KEF) ke yi.

Sanata Lawal Adamu Usman ya soki ƙungiyar dattawan kan neman a yi masa kiranye daga majalisar dattawa saboda zargin rashin ƙwarewa.

Sanata Lawal Adamu Usman ya yi martani kan shirin yi masa kiranye
Sanata Lawal Adamu Usman ya caccaki kungiyar KEF Hoto: Sen Lawal Adamu Usman
Asali: Facebook

Sanatan ya yi wannan martanin ne a cikin wata sanarwa da babban mai taimaka masa na musamman, Segun Olatunji, ya fitar a ranar Talata, cewar rahoton jaridar The Punch.

Kara karanta wannan

Shugaban NYSC ya fadi lokacin fara biyan masu yi wa kasa hidima N77,000

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Idan ba ku manta ba, shugaban ƙungiyar (KEF), Inuwa Rigasa, ya yi barazanar yi wa sanatan kiranye daga majalisar bisa zargin rashin cika alƙawuran da ya ɗauka a lokacin yaƙin neman zaɓe.

Me sanatan ya ce kan shirin yi masa kiranye

Sai dai a martanin da ya yi, Sanata Lawal Usman ya bayyana maganganun na ƙungiyar KEF a matsayin “abin dariya” da kuma “na yara,” yana mai cewa yana da ayyuka masu yawa a gabansa saboda haka bai da lokacin ɓatawa wajen biye musu.

Sanatan ya nuna cewa ba wannan ne karon farko da KEF ko masu ɗaukar nauyinta suka yi irin wannan barazana ba, inda a baya suka yi hakan a ƙarƙashin ƙungiyar Kaduna Peace and Tranquility Forum (KPTF) tare da ba da wa’adin kwanaki 14.

Ya soki nagartar ƴan ƙungiyar KEF, yana zarginsu da yin aiki don amfanin masu ɗaukar nauyinsu da shugabanninsu, ba don talakawan yankin mazaɓar Kaduna ta Tsakiya ba, rahoton jaridar The Nation ya tabbatar.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Sokoto ta fadi abin da za ta yi wa wadanda gobarar kasuwar Kara ta shafa

Sanata Lawal Adamu ta aikinsa yake yi

“Ina da ayyuka masu muhimmanci na majalisa fiye da shiga cikin gardama marasa tushe da mutanen da ke aiki don cimma burin wasu ƴan siyasa da suke fakewa da su domin su yaƙe ni a siyasance."
"Me ya faru da barazanar da wannan ƙungiya ta yi a baya ta yi mani kiranye daga majalisa tare da ba da wa’adin kwanaki 14 a ƙarƙashin inuwar Kaduna Peace and Tranquility Forum (KPTF)?"
"Sake dawo wannan barazana daga waɗannan mutanen a ƙarƙashin sabon sunan (KEF) abin dariya ne kuma abin mamaki."
“Ina kira ga jama'ar mazaɓar Kaduna ta Tsakiya da ka da su bari a yaudare su da ƙaryar da ake yadawa a kai na daga waɗannan dattawan da ake kira na Kaduna."
"Domin ba su da nagartar nuna cewa suna son talakawan mazaɓar, alhali suna aikata ayyuka marasa kyau domin cika burin masu ɗaukar nauyinsu da shugabanninsu."

Kara karanta wannan

Ganduje ya yi wa Kwankwaso shagube, ya yi barazanar kwace Kano a zaben 2027

- Lawal Adamu Usman

Sanatan PDP ya sha da ƙyar a Kaduna

A wani labarin kuma, kun ji cewa Sanatan da ke wakiltar Kaduna ta Tsakiya a majalisar dattawa, Lawal Adamu Usman, ya tsallake rijiya da baya daga hannun ƴan bindiga.

Sanata Lawal Adamu Usman ya bayyana cewa ya sha da ƙyar bayan wasu mahara sun farmake shi lokacin da yake tafiya a kan titi.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng