Jerin Shugabannin Miyetti Allah da Aka Kashe a Shekara 5 da Suka Gabata
FCT, Abuja - A cikin ƴan shekarunnan da suka gabata, an kashe shugabannin ƙungiyar Miyetti Allah (MACBAN), da dama a Najeriya.
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Na baya-bayan nan shi ne Alhaji Amadu Surajo, muƙaddashin shugaban MACBAN na Katsina, wanda aka kashe a gidansa da ke ƙauyen Mai Rana.
Shugabannin Miyetti Allah da aka kashe
Wannan rahoto ya kawo sunayen wasu shugabannin ƙungiyar Miyetti Allah bakwai da aka kashe daga 2019 zuwa 2025.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Da yawa daga cikin shugabannin na ƙungiyar Miyetti Allah da aka kashe a tsakanin 2019 zuwa 2025, ana zargin ƴan bindiga ne suka raba su da duniya.
1. Amadu Surajo
A daren ranar Asabar, 4 ga watan Janairu, 2025, wasu ƴan bindiga suka kashe Amadu Surajo, shugaban MACBAN na Katsina, tare da wasu mutane biyu, cewar rahoton jaridar The Guardian.
Lamarin ya faru ne lokacin da ƴan bindigar suka farmaki ƙauyen Mai Rana a ƙaramar hukumar Kusada ta jihar Katsina.
Rahotanni sun bayyana cewa ƴan bindigan sun kuma sace matansa biyu da yarsa guda ɗaya, wacce aka ɗalibar jami’a ce.
2. Yakubu Muhammad
A watan Yuli na shekarar 2024, aka kashe Yakubu Muhammad, shugaban matasa na ƙungiyar MACBAN a ƙaramar hukumar Bassa, jihar Plateau.
Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa an harbe shi a wajen shan shayi a yankin Jebu na ƙaramar hukumar.
Kafin rasuwarsa, Muhammad ya kasance mamba a wani kwamiti na zaman lafiya mai mutum 57 da sojojin Najeriya suka kafa, don sasanta rikicin manoma da makiyaya a sassan Mangu, Barkin Ladi, Riyom, Jos ta Kudu da Bassa.
3. Adamu Aliyu
A watan Afrilun shekarar 2022, wasu ƴan bindiga suka kashe Adamu Aliyu, shugaban ƙungiyar MACBAN na ƙaramar hukumar Gwagwalada a babban birnin tarayya Abuja.
Adamu Aliyu da wasu mutane huɗu sun rasa rayukansu a wani hari da ƴan bindigan suka kai a yankin Dako, kusa da ƙauyen Dobi.
4. Abubakar Abdullahi
A watan Satumba na shekarar 2021, ƴan bindiga sun kashe shugaban ƙungiyar MACBAN na ƙaramar hukumar Lere a jihar Kaduna, Abubakar Abdullahi, a wani hari.
Rahotanni sun ce maharan sun kutsa gidansa a Kaduna, sannan suka tilasta masa ya tara N250,000 daga mahautan da ke yankinsa kafin su kashe shi.
Jagororin ƙungiyar MACBAN na jihar Kaduna sun tabbatar da lamarin a wata sanarwa.
5. Mohammed Hussain
A watan Afrilu na 2021, wasu ƴan bindiga da ake zargin ƴan ta’adda ne sun kashe Mohammed Hussain, shugaban MACBAN na jihar Nasarawa, a kasuwar Garaku da ke ƙaramar hukumar Kokona.
Rundunar ƴan sandan jihar Nasarawa ta tabbatar da aukuwar lamarin a wata hira da ta yi da manema labarai, cewar rahoton jaridar The Punch.
6. Mohammed Umar
A daren Juma’a, 2 ga watan Afrilu, 2021, maharan da suka kashe Mohammed Hussain sun kuma kashe Mohammed Umar, shugaban MACBAN na ƙaramar hukumar Toto a jihar Nasarawa.
Shi ma ƴan bindigan sun kashe shi ne a kasuwar Garaku da ke ƙaramar hukumar Kokona, rahoton tashar Channels tv ya tabbatar.
Bayan gwajin likita ya tabbatar da rasuwarsu, an adana gawarwakinsu a ɗakin ajiyar gawa na Anthony Memorial Mortuary.
7. Alhaji Saidu Kolaku
A watan Agusta na shekarar 2019, wasu ƴan bindiga sun kashe Alhaji Saidu Kolaku, shugaban ƙungiyar MACBAN na jihar Adamawa.
Maharan sun kai masa hari a gidansa da ke Sabon Pegi, ƙaramar hukumar Moyo Belwa, inda suka harbe shi har lahira.
Ƴan uwansa sun ce kisan nasa na iya zama ramuwar gayya, kasancewar yana taimaka wa jami’an tsaro wajen kamo masu garkuwa da mutane da sauran masu aikata laifuka a jihar Adamawa.
Kotu ta amince a tsare shugaban Miyetti Allah
A wani labarin kuma, kun ji cewa wata babbar kotun tarayya da ke birnin Abuja ta amince da buƙatar hukumar DIA ta tsare shugaban ƙungiyar Miyetti Allah, Bello Bodejo.
Kotun ta amince hukumar leƙen asiri ta sojoji (DIA) ta ci gaba da tsare Bello Bodejo da wasu mutum shida da ake tuhumarsu a tare, har na tsawon kwanaki 60.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng