Sanata Barau Ya Dauko Salon Kwankwasiyya, Zai Dauki Nauyin Karatun Dalibai 300
- Sanata Barau Jibrin ya sanar da bayar da tallafin karatun digiri na biyu ga dalibai 300 bayan tura 70 zuwa kasar Indiya karatun digirin digirgir
- Dalibai daga Jihar Kano ne za su amfana da wannan shirin karkashin gidauniyar Barau I Jibrin Foundation (BIJF)
- Shirin zai mayar da hankali kan ci gaban kimiyya da fasaha, tsaron yanar gizo da sauran bangarorin ilimin zamani da za su tallafi matasa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Kano - Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau I. Jibrin ya fitar da sabon shirin tallafin karatu ga dalibai 300 domin karatun digirgi a manyan jami’o’in Najeriya.
Wannan ya biyo bayan tura dalibai 70 zuwa kasar Indiya domin karatun digirin digirgir, wanda aka kaddamar a ranar 29 ga Disamba, 2024, ta filin jirgin saman Malam Aminu Kano.
Legit ta gano yadda shirin zai gudana ne a cikin wani sako da Sanata Barau Jibrin ya wallafa a shafinsa na Facebook.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Daily Trust ta wallafa cewa mai ba Sanatan shawara kan harkokin yada labarai, Ismail Mudashir, ya ce gidauniyar Barau I Jibrin (BIJF) ce za ta dauki nauyin shirin.
Manufar Gidauniyar Barau I Jibrin
Gidauniyar Barau I Jibrin tana da burin tallafa wa matasan Kano wajen samun ingantaccen ilimi da horo domin gina dan Adam a fannonin kimiyya da fasaha.
Sakataren Kwamitin Tallafin Karatu na BIJF, Dr Maikudi Lawan, ya bayyana cewa shirin zai bai wa dalibai damar kwarewa a fannonin bincike da ci gaban ilimi.
Ya ce, shirin yana nufin tallafa wa matasa ne domi gina masana da za su taka rawar gani a fannoni daban-daban na kimiyya da fasaha.
A karkashin shirin, za a tura dalibai jami'o'i kamar haka:
- Jami'ar Bayero ta Kano
- Jami'ar Ahmadu Bello ta Zariya
- Jami'ar Ibadan
- Jami'ar Nsukka
- Jami'ar Obafemi Awolowo University ta Ile-Ife
- Jami'ar Lagos
Barau zai cigaba da tallafawa daliban Kano
Sanata Barau Jibrin ya bayyana cewa shirin tallafin karatun zai zama wani karin ci gaba bayan nasarar da ya samu a shirin tallafin karatu na kasashen waje.
A cewarsa, sun fara da tura dalibai 70 zuwa Indiya domin ci gaba da karatunsu, kuma yanzu sun mayar da hankali kan samar da damar karatu a nan gida ga dalibai 300.
Shirin tallafin karatun cikin gida zai taimaka wajen rage gibin da ake da shi a fannin ilimi tare da bunkasa harkokin bincike da fasaha.
Muhimmancin shirin ga matasan Kano
Sanata Barau ya kara da cewa horar da matasa a irin wadannan fannonin zai taimaka wajen cike gibin da ake da shi a wajen aiki da kuma bunkasa tattalin arzikin kasa.
Shirin tallafin karatun ya samu karbuwa daga dalibai da iyayensu, inda aka bayyana cewa yana nuni da irin jajircewar Sanata Barau wajen ganin matasa sun samu cigaba mai dorewa.
Sanarwar ta tabbatar da cewa Sanata Barau zai ci gaba da aiwatar da irin wadannan shirye-shirye domin ciyar da ilimi gaba a Kano da Najeriya baki daya.
Barau ya raba tallafi ga 'yan sanda
A wani rahoton, kun ji cewa mataimakin shugaban majalisar dattawa, Sanata Barau Jibrin ya tallafawa 'yan sanda da abubuwan hawa.
Hakan na zuwa ne yayin da gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya raba tallafin motoci da abubuwan hawa ga 'yan sanda a jihar.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng