Tirkashi: Shugaban Ƙaramar Hukuma a Jihar Kano Ya Naɗa wa Kansa Hadimai 60

Tirkashi: Shugaban Ƙaramar Hukuma a Jihar Kano Ya Naɗa wa Kansa Hadimai 60

  • Shugaban ƙaramar hukumar Nasarawa, Hon. Yusuf Imam, ya amince da nadin hadimai 60 domin yin aiki a bangarori daban-daban
  • A cikin wata sanarwa daga sakataren karamar hukumar, an ce Hon. Yusuf ya yi nade-naden ne domin inganta gudanarwar Nasarawa
  • An rahoto cewa wadanda aka nada sun hada da mataimaka na musamman, masu kawo rahoto, daraktoci da ma direban ciyaman

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Kano - Shugaban karamar hukumar Nasarawa a jihar Kano, Yusuf Imam, wanda aka fi sani da 'Ogan Boye,' ya amince da naɗin hadimai 60.

A cewar wata wasika da sakataren karamar hukumar, Ado Muhd Hotoro ya fitar, sababbin nade naden na daga cikin yunƙurin inganta Nasarawa.

Shugaban karamar hukuma a Kano ya nada hadimai 60
Shugaban karamar hukumar Nasarawa a Kano ya nada hadimai 60. Hoto: Aminu Ogan Boye
Asali: Facebook

Kano: Ciyaman ya nada hadimai 60

Wasikar, mai ɗauke da kwanan watan 6 ga Janairu, 2024, ta bayyana cewa Ogan Boye ya yi nadin ne domin ci gaban al'ummar Nasarawa, inji rahoton Daily Trust.

Kara karanta wannan

Sokoto: Sakataren gwamnati ya shiga jarabawa, 'yarsa da jikoki 3 sun rasu lokaci daya

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Daga cikin wadanda aka naɗa akwai 'masu ba da rahoto na musamman' guda 18 domin kula da sassa daban-daban, kasuwanni da cibiyoyin lafiya.

Haka kuma, shugaban karamar hukumar ya nada 'manyan mataimaka,' 'shugaban tsara harkokin gwamnati,' 'babban jami'in tsare-tsare,' da shugabannin manyan sassa takwas.

"An nada hadiman bisa cancanta" - Ado Hotoro

Wasikar ta jaddada cewa an yi naɗin ne bisa cancanta, gaskiya da ƙwazon da mutanen suka nuna domin tabbatar da shugabanci mai nagarta a karamar hukumar.

Hakanan, an nuna tabbacin cewa waɗanda aka naɗa za su gudanar da ayyukansu bisa ƙwazo don cimma burin Ogan Boye na ci gaban karamar hukumar Nasarawa.

Hassan Shehu Adam- Twins, mai ba shugaban karamar hukumar shawara kan watsa labarai, ya tabbatar da wadannan nade nade a shafinsa na Facebook.

Jerin sunayen wadanda aka ba mukamai

Mai magana da yawun Hon. Yusuf Imam, ya fitar da sunayen wadanda aka nada kamar haka:

Kara karanta wannan

Abba ya yi sababbin nade nade, mutum 5 sun samu manyan mukamai a gwamnatin Kano

  1. Jamil D. Attahir: sakatare na musamman (PPS).
  2. Rabilu Muhammad Gama: mataimaki na musamman kan rubuce-rubuce.
  3. Kabiru Ishaq Hannafi: mataimaki na musamman kan harkokin cikin gida.
  4. Ahmad Hussaini Nuhu: mataimaki na musamman kan ayyuka na musamman.
  5. Hassan Shehu Adam: mataimaki na musamman kan kafofin watsa labarai I.
  6. Comrd Muhd Habib: mataimaki na musamman kan kafofin watsa labarai II.
  7. Habibu Adamu Abubakar: mataimaki kan rubuce-rubuce ga mataimakin shugaban ƙaramar hukuma.
  8. Ahmad Aminu Sunusi: mataimaki kan harkokin cikin gida ga mataimakin shugaban ƙaramar hukuma.
  9. Kamal Muhammad Adam: mataimaki kan rubuce-rubuce ga sakataren ƙaramar hukuma.
  10. Farouq Garba: mataimaki kan al’amuran cikin gida ga sakataren ƙaramar hukuma.
  11. Jamilu Sa’id: babban mai kula da al’amuran karamar hukuma I.
  12. Salisu Garba: babban mai kula da al’amuran karamar hukuma zII.
  13. Shamsu Yahaya Abdullahi: mataimaki na musamman kan hotuna.
  14. Halima Abubakar: mataimakiya ta musamman kan harkokin mata.
  15. Auwalu Abdullahi: babban mai kula da tsare-tsare.
  16. Khadija Idris: babbar darakta kan harkokin jin kai.
  17. Abdul’Aziz Badamasi: babban darakta kan tattalin arziki na zamani.
  18. Sharif Nazir Hassan: babban darakta kan filaye da tsare-tsare
  19. Sunusi Abdullahi Ya’u: babban darakta kan harkokin cikin gida.
  20. Barrister Umar Shehu Kawaji: lauyan ƙaramar hukuma.
  21. Hon. Dalha Yusuf Babban Gawo: babban darakta kan tsare-tsaren ayyukan ci gaba.
  22. Dr. Garba Miko Dakata: babban darakta kan harkokin siyasa.
  23. Hon. Sani Jibrin SK: babban darakta kan harkokin ƙungiyoyi.
  24. Usman M.K. Giginyu: babban darakta kan ayyuka.
  25. Jazuly Isah Fashion: babban darakta kan kasuwanni.
  26. Muhd Yusuf Hamza: mataimaki na musamman kan samar da ayyukan yi.
  27. Hon. Joshua Gawuna: mataimaki na musamman kan kabilu.
  28. Yusuf Hassan Gote: mataimaki na musamman kan ƙungiyoyi
  29. Abdullahi Dauda: mataimaki na musamman kan gidajen mayanka (kwata).
  30. Mustapha Muhd Adam: mataimaki na musamman kan ayyuka da sa ido.
  31. Sabo A. Abdullahi: mataimaki na musamman kan kasuwar 'Yankaba.
  32. Hon. Muhd Hussain: mataimaki na musamman kan kabilanci da jinsi.
  33. Isma’il Abdullahi Gwagwarwa: mataimaki na musamman kan tattara haraji.
  34. Sa’idu Muhd: mataimaki na musamman kan kididdiga.
  35. Umar Sunusi Umar: mataimaki na musamman kan zuba jari da kadarori.
  36. Safiyanu Ibrahim Muhd: mataimaki na musamman kan tashar titin Hadeja.
  37. Nura Bala: babban mataimaki na musamman kan tashar titin Hadeja.
  38. Rabi’u Abdullahi Shu’aibu: babban mataimaki na musamman kan kasuwar 'Yankaba.
  39. Isma’il Muhd Tafida: mataimaki na musamman kan kasuwar Dakata.
  40. Lawan Abubakar Muhd: mataimaki na musamman kan kasuwar Gama.
  41. Adamu Sa’idu: mai rahoto na musamman kan kasuwar Gama.
  42. Ummalkhairi Yusuf: mai rahoto na musamman kan asibitin Gwagwarwa.
  43. Shafa’atu Yusuf: mai rahoto na musamman kan asibitin Kaura Goje.
  44. Fiddausi Sani: mai rahoto na musamman kan asibitin Hotoron Arewa.
  45. Basira Ahmad: mai rahoto na musamman kan asibitin Gama.
  46. Zakiya Yunusa: mai rahoto na musamman kan asibitin Dakata.
  47. Fatima Dayyaba Haruna: mai rahoto na musamman kan sashen jama’a na Nasarawa..
  48. Lawan Ubale: mai rahoto na musamman kan kasuwar Dakata.
  49. Gaddafi Sulaiman Hassan: mai rahoto na musamman kan ayyuka.
  50. Salisu Muhd Nasir: mai rahoto na musamman kan sashen noma da albarkatun ƙasa.
  51. Aminu Adamu: mai rahoto na musamman kan ayyuka da sa ido.
  52. Shu’aibu Abdullahi: mai rahoto na musamman kan sashen lafiya.
  53. Yahaya Umar Gawuna: mai rahoto na musamman kan sashen ruwa.
  54. Bashir Abdurrazak: mai rahoto na musamman kan ilimi.
  55. Mustapha Sani: mai rahoto na musamman kan kasuwar 'Yankaba.
  56. Barrister Adamu Muhd Gwagwarwa: mai kula da doka.
  57. Hafsat Muhd Idris: mai rahoto na musamman kan asibitin Sauna.
  58. Auwalu Sani: direban shugaban ƙaramar hukuma.
  59. Tanimu Isa Oga: mai rahoto na musamman kan asibitin Hotoron Kudu.
  60. Muhammad Idris Muhammad: mai rahoto na musamman kan sashen PRS.

Kara karanta wannan

Peter Obi ya ziyarci IBB, ya bayyana abubuwan da suka tattauna a kan Najeriya

Sani Danja ya rasa takarar ciyaman a Kano

A wani labarin, mun ruwaito cewa fitaccen mawaki kuma jarumin Kannywood, Sani Musa Danja ya gaza samun tikitin takarar ciyaman na Nasarawa a karkashin NNPP.

An rahoto cewa wakilan jam'iyyar NNPP sun zabi Hon. Yusuf Imam (Ogan Boye) a matsayin dan takarar ciyaman na karamar hukumar da ke Kano.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.