Sheikh Ahmad Gumi Ya Yi Magana kan Tsaro yayin da Sojoji ke Kokarin Cafke Turji
- Malamin addinin Musulunci, Ahmad Gumi ya bayyana cewa kafa Ma’aikatar Kula da Dabbobi za ta taimaka wajen magance matsalar ‘yan bindiga
- Sheikh Gumi ya yabawa gwamnan Kaduna kan tattaunawar sulhu da ake yi da ‘yan bindiga, wanda ya haifar da zaman lafiya a wasu yankuna
- Malamin ya ja hankalin gwamnati kan matsalolin tattalin arziki da fatara, yana mai cewa rashin wadata yana kara ta’azzarar matsalolin tsaro a kasa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Kaduna - Sheikh Ahmad Abubukar Gumi ya ce sabuwar Ma’aikatar Kula da Dabbobi da shugaba Bola Tinubu ya kirkira za ta iya taka rawar gani wajen magance matsalolin tsaro.
Sheikh Ahmad Gumi ya yi bayanin ne yayin karbar bakuncin tsohon Ministan Wasanni, Solomon Dalung, a gidansa da ke Kaduna a ranar Lahadi.
A bidiyon da ya wallafa a Facebook, Sheikh Gumi ya ce kafa ma’aikatar na iya taimaka wa makiyaya wajen samun cigaba, wanda hakan zai rage rikice-rikicen manoma da makiyaya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gumi: 'Tasirin ma’aikatar kula da dabbobi'
Sheikh Ahmad Gumi ya bayyana cewa Ma’aikatar Kula da Dabbobi da aka kirkira a shekarar 2024 za ta kawo sauyi sosai idan aka gudanar da ita ba tare da saka siyasa ba.
Ya ce idan 'yan bindiga suka samu ci gaba wajen samun hanyoyi da abubuwan more rayuwa, akwai yiwuwar su ajiye makamai.
Malamin ya kuma yi nuni da cewa 'yan bindigar daji suna daukar mazauna birni a matsayin makiya, ciki har da abokan zamansu Fulani.
Sheikh Gumi ya tabo batun sulhu da ‘yan bindiga
Sheikh Gumi ya yabawa Gwamnan Kaduna, Uba Sani, kan kokarin tattaunawar sulhu da ‘yan bindiga.
Ya ce;
“A Birnin Gwari, an samu nasarar dawo da mutane gonakinsu da kuma bude kasuwanni.”
Sheikh Gumi ya yi kira ga gwamnati da ta yi amfani da mutane da suka fahimci al’adun ‘yan bindiga domin tattaunawa tare da kawo karshen matsalolin tsaro.
Premium Times ta wallafa cewa malamin ya ce rashin ilimi da dabi’ar makiyaya ke sa wasu mutane na amfani da 'yan bindigar wajen cimma burinsu na son kai.
Matsalar tattalin arziki da tasirinta ga tsaro
Sheikh Gumi ya ce tsauraran manufofin tattalin arziki na gwamnatin tarayya suna kara matsalar tsaro.
Malamin ya ce ba daidai ba ne gwamnati ta kasance mai arziki, alhali jama’arta na cikin talauci, a kan haka ya ce ya kamata a koma tsarin da zai tallafa wa talakawa.
Ya yi kira da a zuba jari a fannin koyar da sana’o’i domin tallafa wa matasa su fuskanci tsarin tattalin arziki na zamani.
Haka zalika malamin ya ce yawanci masu kunna wutar rikici a Najeriya 'yan kasar waje ne saboda mummunar manufa da suke da ita.
Barazanar kungiyar Lakurawa a Najeriya
Tsohon Minista Solomon Dalung ya bayyana damuwa kan bullar sabuwar kungiyar ta’addanci mai suna Lakurawa.
Ya ce Lakurawa ba ‘yan Najeriya ba ne, kuma ba Fulani ba ne. Amma suna kara samun karfi, suna mamaye wurare tare da gina rijiyoyi domin jan hankalin matasa.
Sojojin Najeriya sun firgita Bello Turji
A wani rahoton, kun ji cewa sojojin Najeriya sun kai zafafan hare hare kan 'yan ta'adda da suke da alaka da Bello Turji.
Sojojin rundunar Operation Fansan Yamma sun bayyana cewa a yanzu haka Bello Turji ya firgita yana buya a ramuka kamar beran daji.
s
Asali: Legit.ng