Yarbawa 'Miliyan 60' Sun Dage sai An Raba Najeriya, Sun Nemi Taimakon Ƙasar Waje
- Farfesa Banji Akintoye ya dage kan cewa ba za su janye daga kudurinsu na neman kafa ƙasar Yarbawa mai cin gashin kai ba
- Ya bayyana cewa kusan mutane miliyan 60 na kabilar Yarbawa a gida da ƙetare suna goyon bayan kafa ƙasarsu ta kansu
- Farfesa Akintoye ya jaddada cewa suna neman cin gashin kai bisa doka da lumana, ya ce sun nemi taimakon wata kasar waje
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Ekiti - Shugaban ƙungiyar da ke rajin 'yancin Yarbawa, Farfesa Banji Akintoye, ya ce ba za su janye daga neman kafa ƙasar Yarbawa ba.
Farfesa Akintoye ya bayyana cewa mutane kusan miliyan 60 na Yarbawa a gida da ƙetare suna goyon bayan kafa ƙasar Yarbawa mai cin gashin kai.
Yarbawa na son ballewa daga Najeriya
Da yake magana da jaridar The Punch a ranar Litinin, Akintoye ya ce:
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
“Ba za mu ja da baya ba. Dole mu balle daga Najeriya ko kuwa muna ji muna gani ƙasarmu ta lalace."
Ya ci gaba da cewa:
“Ba ku ji muryarmu a tituna ba? A yanzu babu ja da baya a neman kafa kasar Yarbawa, za mu tabbatar da mun yi nasara.
Shugaban kungiyar ya ce akwai Yarbawa kusan miliyan 55 zuwa 60 a Najeriya don haka suna son kafa ƙasarsu ta kansu.
Yarbawa sun nemi taimakon Birtaniya
Farfesa Akintoye ya yi imanin cewa Yarbawa na ballewa za a nemi Najeriya a rasa, amma idan sauran kabilu na son zama a Najeriya, ba matsala gare su.
Da aka tambayi Akintoye game da wasikar da suka rubuta ga gwamnatin Birtaniya a bara, ya ce sun samu tabbacin cewa ana duba bukatarsu.
“Mun sani tun farko cewa muna hulda da daya daga cikin gwamnatoci mafi ƙarfi a duniya, ba za mu samu amsa a wata daya ko biyu ba."
“Amma mun samu wani nau’in sakon da ya nuna tabbacin cewa ana duba wasikar ta mu. Mun samu wannan tabbacin ne bayan mun mika wasikar.”
- Farfesa Akintoye.
"Wasikarmu na daga hankalin Najeriya" - Akintoye
Farfesa Akintoye ya ci gaba da cewa:
“Gwamnatin Birtaniya ce. Ba za mu yi sauri da su ba. Amma jinkirin bai nuna cewa ba su dauki batun mu da muhimmanci ba."
A makamanciyar wasikar da suka aika wa gwamnatin Najeriya, Farfesa Akintoye ya ce suna da hujjar cewa wasikar na haddasa tashin hankali a gwamnati.
“Eh, sun fara aiki a kai. Mun samu tabbacin cewa suna aiki a kan bukatarmu kuma mun ga shaidar cewa wasikar tana tada musu hankali.”
- Farfesa Akintoye.
"Yarbawa na da 'yancin kafa kasa" - Akintoye
Farfesa Akintoye ya ce Yarbawa na da 'yancin kafa kasarsu, yana mai cewa:
“Akwai abubuwa da dama masu muhimmanci da za a duba. Na farko, muna da ‘yancin neman cin gashin kan jama’armu.
“Dokar Majalisar Ɗinkin Duniya kan haƙƙin mutanen asali ta tabbatar da cewa kowace ƙabila tana da ‘yancin cin gashin kanta.
“Dokar ta ce dole ne kabilar ta yi hakan cikin lumana ba tare da tashin hankali ko barazana ba. Kuma muna kiyaye wannan dokar sosai."
Abin da ya jawo neman kafa kasar Yarbawa
Tun da fari, mun ruwaito cewa Farfesa Banji Akintoye ya bukaci a ware ƙasa ta musamman ga Yarbawa domin magance matsalolin da suke fuskanta a Najeriya.
Ya ce yawan kashe-kashen mutane da rikicin makiyaya a Kudancin Najeriya ya sa bai dace a jinkirta wannan ƙuduri ba.
Akintoye ya yi kira ga sarakuna da gwamnonin yankin su goyi bayan wannan ƙuduri don inganta tsaro da haɓaka tattalin arzikin Yarbawa.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng