Kudin Hajji: Gwamna Abba Ya Nemawa Musulmai Alfarma a wajen Tinubu
- Gwamna Abba Kabir Yusuf na Jihar Kano ya yi kira ga gwamnatin tarayya ta rage farashin kujerar Hajjin 2025 saboda matsalolin tattalin arziki
- Jihar Kano ta raba Naira miliyan 375 ga mahajjatan 2023 a matsayin kudin da aka dawo da su daga Saudiyya sakamakon matsalar wutar lantarki
- Gwamnan ya yabawa Hukumar Alhazai ta Kasa (NAHCON) da gwamnatin Saudiyya kan kyakkyawan shugabanci da kulawa da al’umma
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar - Gwamna Abba Kabir Yusuf na Jihar Kano ya roki gwamnatin tarayya da ta rage farashin kujerar hajjin 2025 domin saukaka wa al’ummar kasa da ke fama da matsalolin tattalin arziki.
Ya bayyana haka ne yayin wani taro da Hukumar Alhazan Kano ta shirya domin raba kudin da Saudiyya ta dawo da su sakamakon matsalar wutar lantarki a lokacin aikin hajjin 2023.
Bayanin gwamnan ya fito ne daga bakin mai magana da yawunsa, Sanusi Bature Dawakin Tofa, a wata sanarwa da ya wallafa a Facebook ranar Litinin.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An raba N375m ga mahajjatan Kano
Gwamna Abba Kabir Yusuf ya yabawa gwamnatin Saudiyya bisa dawo da kudin da ta yi wa mahajjatan 2023 daga jihar Kano saboda rashin samar musu da lantarki a wasu lokuta.
Abba Kabir ya ce kyautatawar ta nuna kulawar gwamnatin Saudiyya ga al’umma, inda ya kara da cewa zai aika wasiƙar godiya zuwa ofishin jakadancin Saudiyya da ke Kano.
A cewar Babban Daraktan Hukumar Alhazai ta Jihar Kano, Alhaji Laminu Rabiu Danbaffa, adadin kudin da aka dawo da su ta hannun NAHCON domin rabawa mahajjatan Kano ya kai N375m.
Bukatar rage kudin kujerar Hajjin 2025
Da yake magana a wurin taron, aAbba Kabir ya roki gwamnatin tarayya da ta rage farashin kujerar hajjin 2025 domin rage nauyin da yake kan al’umma.
Gwamnan ya ce;
“A matsayina na mai kishin al’umma, ina rokon gwamnatin tarayya ta yi la’akari da halin tattalin arziki da al’umma ke ciki,
Ta rage farashin hajji domin sauƙaƙawa jama’a damar yin wannar ibada mai muhimmanci.”
Leadership ta rahoto cewa gwamnan ya yaba wa Hukumar Alhazai ta Kasa (NAHCON) bisa gudanar da ayyuka cikin adalci da tsari, musamman kan biyan kudin a kan lokaci.
Shirye-shiryen Hajjin 2025
Gwamnan ya bayyana cewa ya ziyarci Saudiyya a makonnin da suka gabata domin yin Umara da kuma fara shirin hajjin 2025 da gano wuraren da gwamnatin jihar za ta kara tallafawa mahajjata.
Ya kuma yaba wa Hukumar Alhazai ta Jihar Kano bisa kyakkyawan jagoranci da gudanar da aikin hajjin 2023, wanda aka yarda da shi a matsayin mai inganci a kasar nan.
Mataimakin Gwamnan Jihar Kano, Aminu Abdulsalam Gwarzo, wanda ya jagoranci tawagar mahajjatan 2024, ya gode wa gwamnan bisa goyon bayan da ya bayar ga mahajjata.
Abba ya nada manyan mukamai 5
A wani rahoton, kun ji cewa gwamnan jihar Kano, Abba kabir Yusuf ya yi sababbin nade nade a gwamnatinsa.
Gwamna Abba Kabir Yusuf ya nada manyan mukamai har guda biyar domin ba al'umma damar taimaka masa wajen kawo cigaba.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng