Ma’aikata 1,000 da CBN Ya Sallama Sun Maka Shi Kotu, An Nemi Diyya Mai Tsoka

Ma’aikata 1,000 da CBN Ya Sallama Sun Maka Shi Kotu, An Nemi Diyya Mai Tsoka

  • Tsofaffin ma’aikatan sun zargi bankin CBN da karya dokokin cikin gida da na kwadago da jin ta baki kafin sallamarsu daga aiki
  • Ma’aikatan sun bayyana cewa tsarin sallamar ba bisa ka’ida ba ne, tare da neman kotu ta ayyana shi a matsayin haramtacce
  • Mai shari’a O. A. Osaghae ya bukaci bangarorin biyu su nemi mafita ta hanyar sulhu, yayin da aka dage shari’ar zuwa Janairu

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT Abuja -Tsofaffin ma’aikatan Babban Bankin Kasa (CBN) da aka sallama daga aiki a shekarar 2024 sun kai karar bankin a Kotun Kwadago ta Kasa da ke Abuja.

Tsofaffin ma’aikatan, a cikin wata karar da suka shigar ranar 4 ga Yuli, 2024, sun gabatar da matsaloli daban-daban domin kotu ta yanke hukunci a kansu.

Kara karanta wannan

Abin fashewa ya tarwatse a jihar Ribas, ya rutsa da mutane 20

Banki
Tsofaffin ma'aikatan CBN sun garzaya kotu Hoto :CBN
Asali: Facebook

Jaridar Premium Times ta wallafa cewa ma’aikatan su na bukatar kotu ta tambaya dalilin hana su kare kansu a gaban bankin kafin sallamarsu bai saba doka ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An zargi bankin CBN da karya doka

Jaridar Punch ta ruwaito cewa tsofaffin ma’aikatan sun yi ikirarin cewa CBN ya karya dokokin cikin gida, dokokin kwadago na Najeriya da kuma tauye hakkinsu na aiki.

Sun kuma ce tsarin sallamar da aka aiwatar a ranar 5 ga Afrilu, 2024, ya ci karo da ka’idoji da dokokin aiki na CBN da kuma sashe na 36 na Kundin tsarin mulkin Najeriya.

Ma’aikatan sun kara da cewa an sallamme su na tare da jin ta bakinsu ba kamar yadda doka ta tanada ba, inda suke zargin an sallame sub a bisa ka’ida ba.

Bukatar tsofaffin ma’aikatan CBN a Kotu

Tsofaffin ma’aikatan na CBN sun bukaci Kotun kwadago da ke zamansa a Abuja da ta ayyana cewa sallamar aikin da aka yi musu ba ta halatta ba kuma ta sabawa doka.

Kara karanta wannan

APC: El Rufa’i ya bayyana matsayinsa kan jita jitar sauya sheka

Haka zalika, suna bukatar kotu ta ba da umarnin a dawo da su kan mukamansu nan take tare da biyan su albashi da sauran alawus daga ranar da aka sallame su.

Haka kuma, tsoffin ma’aikatan suna neman kotu ta umarci CBN ta biya su diyyar Naira biliyan 30 saboda damuwa ta tashin hankali da tauye masu hakki da aka yi.

Sannan suna neman karin Naira miliyan 500 don biyan kudin wannan shari’ar.

Alkali ya ba bankin CBN shawara

A zaman farko na sauraren wannan kara ranar 20 ga Nuwamba, 2024, kotu ta bukaci bangarorin da ke cikin wannan shari’ar su yi kokarin samun sulhu a tsakaninsu.

CBN, karkashin jagorancin tawagar lauyoyi da Inam Wilson (SAN) ke jagoranta, ya sanar da kotu cewa sun shigar karar kin amincewa da bukatar tsofaffin ma’aikatan.

Daga bisani, Mai shari’a Osaghae ya dage cigaba da sauraren karar zuwa ranar 29 ga Janairu, 2025, domin jin ƙin amincewar da wanda ake kara ya gabatar.

Kara karanta wannan

Tinubu na ganin sabuwar matsala daga Arewa, dattawa sun ƙi yarda da gyaran haraji

CBN ya yi bayanin korar ma'aikata

A wani labarin, mun ruwaito cewa babban bankin Najeriya (CBN), ya sallami ma’aikata sakalla 1,000 daga bakin aiki a cikin rukuni hudu tsakanin watan Maris zuwa watan Mayu a 2024.

Bankin ya bayyana ware makudan kudi da zai biya a matsayin kudin sallama ga tsofaffin ma’aikatan, inda ya shaida wa majalisar dokoki cewa babu ma'aikacin da aka yi wa dole.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.