Rikici Ya Ɓarke Tsakanin Gwamna a Arewa da Mai Martaba Sarki? Bayanai Sun Fito

Rikici Ya Ɓarke Tsakanin Gwamna a Arewa da Mai Martaba Sarki? Bayanai Sun Fito

  • Sarkin Ilorin, Mai martaba Alhaji Ibrahim Sulu-Gambari ya musanta rahoton da ke cewa ya samu saɓani da gwamnan Kwara, AbdulRahman AbdulRazaq
  • Mai taimakawa sarki na musamman, Dr. Mustala AbdulRaheem ya ce akwai zumunci mai kyau tamkar uba da ɗa tsakanin sarki da gwamna
  • Basaraken ya ce Gwamna AbdulRazaq na amsa kiransa kuma ya bar duk abin da yake yi ya zo wurin da yake cikin awa ɗaya idan ya neme shi

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Kwara - Masarautar Ilorin ta musanta rahoton da wasu kafafen watsa labarai suka wallafa cewa an fara zaman doya da manja tsakanin sarki da Gwamnan Kwara.

Masarautar ta ce babu wani sabani da ya shiga tsakanin Gwamna AbdulRahman AbdulRazaq, da Sarkin Ilorin, Mai martaba Alhaji Ibrahim Sulu-Gambari.

Sarkin Ilorin da Gwamna AbdulRahman AbdulRazaq.
Masarautar Ilorin ta musanta batun samun sabani tsakanin Gwamnan Kwara da sarki Hoto: Abdulrahman Abdulrazaq
Asali: Facebook

Mai taimakawa sarkin Ilorin na musamman, Dr. Murtala AbdulRaheem, shi ne ya yi wannan bayani a wata sanarwa, kamar yadda Leadership ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Abba ya yi sababbin nade nade, mutum 5 sun samu manyan mukamai a gwamnatin Kano

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sanarwar dai na ɗauke da sa hannun mai magana da yawun sarkin, Malam Abdulazeez Arowona, kuma ta shiga hannun manema labarai yau Litinin.

Gwamna da sarkin ilorin sun samu saɓani?

Dr. Murtala AbdulRaheem, ya bayyana dangantakar da ke tsakanin gwamnan da sarkin a matsayin mai kyau kuma mai danƙo wadda take cike da zumunci da mutunta juna.

Hadimin sarkin ya ce:

“Gwamna AbdulRazaq da Sarkin Ilorin, Sulu-Gambari, suna zaman lafiya da zumunci irin na uba da ɗansa.
"Gwamna AbdulRazaq na sama wa mai martaba biza, shirya masa jirage da tafiye-tafiye zuwa ƙasashen waje, har da ba shi kyautauttukan girmamawa."

Sarkin Ilorin ya faɗi alaƙarsa da gwamna

Har ila yau sanarwar ta haƙaito sarkin Ilorin na cewa:

"Gwamna AbdulRazaq ne kadai gwamna da ke amsa kirana nan take kuma ya zo duk inda nake cikin kasa da awa ɗaya ba tare da wani jinkiri ba."
"Akwai kyakkyawar alaƙa tsakanin masarautar Ilorin da ɓangaren shugabancin Kwara karkashin jagorancin gwamnanmu mai son jama’a, Malam AbdulRahman AbdulRazaq.

Kara karanta wannan

Ajali ya yi: Sarki a Najeriya ya gamu mummunan hatsari, Allah ya yi masa rasuwa

Sanarwar ta ƙara da cewa ba ya ga cancanta da ƙaunar talakawa da gwamnan kwara ke nunawa, ya kasance shugaba mai girmama sarakuna da yin shawari da su.

Rahoton da ake yaɗawa ba gaskiya ba ne

Hadimin sarkin ya ce rahoton da jaridar This Day ta wallafa mai taken, "Wa zai sasanta rikicin da ya ɓarke tsakanin sarkin Ilorin da gwamnan Kwara," wani yunƙuri ne na haɗa faɗa.

AbdulRaheem ya ƙara da cewa marubucin labarin bai tuntubi fadar sarkin Ilorin ko gwamnatin Kwara ba domin jin karin bayani kafin ya yaɗa kanzon kuregen.

Ya ce tun hawansa karagar mulki a matsayin gwamnan jihar Kwara, Malam AbdulRahman AbdulRazaq, CON, ya ƙulla zumunci da sarki irin na mahaifinsa tare da mutunta shi.

Gwamnan Kwara ya zama sardaunan Ilorin

A wani rahoton, an ji cewa mai martaba sarkin Ilorin ya naɗawa Gwamna AbdulRahman AbdulRazaq rawanin sarautar sardaunan Ilorin.

Kara karanta wannan

Gwamnan da ake raɗe raɗin zai nemi takarar shugaban ƙasa a 2027 ya kafa tarihi

Wannan naɗi dai ya sa gwamnan Kwara ya zama mutum na biyu da ya riƙe sarautar sardauna a masarautar Ilorin bayan marigayi Alhaji Umar Saro.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262