Gwamnatin Sokoto Ta Fadi Abin da Za Ta Yi Wa Wadanda Gobarar Kasuwar Kara Ta Shafa
- Gwamnatin jihar Sokoto za ta bada tallafi ga mutanen da suka yi asarar dukiya a gobarar da ta auku a kasuwar kara
- Gwamnatin ta kafa kwamitin tantance girman asarar da aka yi gami da samar da matakan kare faruwar hakan a gaba
- Gobarar ta ƙone shaguna da dama gami da lalata injinan niƙa, kayan abinci da sauran kayayyaki masu amfani
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Sokoto - Gwamnatin Jihar Sokoto, ta miƙa saƙon jajantawa da kuma bada tabbacin tallafi ga mutanen da gobara ta shafa a yankin Karar ‘Yan Nika na kasuwar Kara da ke Sokoto.
Gobarar wacce ta ƙone sama da shaguna 50, ta lalata injinan niƙa 132 tare da ƙone kayan abinci masu yawa kamar shinkafa, gero, da wake, lamarin da ya jawo hasarar miliyoyin Naira.
A ƙoƙarin gwamnatin na jajanta wa al’umma, mataimakin Gwamnan Jihar Alhaji Idris Gobir, ya ziyarci wurin don nuna alhini ga waɗanda lamarin ya shafa kamar yadda The Punch ta wallafa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An kafa kwamitin tantance asarar gobara
Yayin ziyarar tasa, ya bayyana cewa an kafa kwamiti don tantance girman asarar da kuma bada shawarar hanyoyin kauce wa irin faruwar hakan a gaba.
“Lokacin hunturu akan samu bushewar yanayi wanda ke ƙara yiwuwar afkuwar gobara. Saboda haka, ya zama dole kowa ya dauki matakan kariya,”
- Alhaji Idris Gobir
Ya tabbatar wa wadanda abin ya shafa cewa gwamnati za ta ɗauki matakin gaggawa da zarar kwamitin ya kammala aikinsa.
Gobarar ta yi matukar shafar ‘yan kasuwar yankin da ma baƙi da ke zuwa, musamman waɗanda kasuwar ita ce hanyar samun abincinsu na yau da kullum.
Hakanan rahoton jaridar The Nation ya bayyana cewa ba iya kasuwar ba ma, har da wasu gidaje da ke maƙwabtaka da ita gobarar ta shafa.
An roƙi gwamnati ta bada tallafi
Shugaban ƙungiyar masu niƙa, Malam Yakubu Bello, ya bayyana alhininsa dangane da asarar da aka yi, yana mai bayyana muhimmancin injinan niƙa wajen ayyukan yau da kullum na kasuwar.
Haka zalika, shugaban ƙungiyar matasa ‘Yan Kasuwa, Alhaji Bashar Nuhu, ya nuna godiya ga mataimakin gwamna saboda ziyarar da ya kai.
Ya bayyana ziyarar a matsayin alamar kulawar gwamnati ga al’ummarta, tare roƙon samun tallafi mai ƙarfi, musamman ga matasa ‘yan kasuwa da abin ya fi shafa.
A na ta ɓangaren, Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Jihar Sokoto (SEMA), ta yi gaggawar kai ɗauki wurin a lokacin da ta samu labari.
Mai bai wa gwamna shawara na musamman kan harkokin agaji Aminu Bodinga, ya yabawa matakan da gwamnati ta ɗauka, yana mai cewa ziyarar mataimakin gwamnan ta zo a kan lokaci kuma za ta yi matuƙar amfani.
Gwamnatin Sokoto ta raba babura da Napep
A wani labarin na daban da Legit ta wallafa a baya, kun ji cewa gwamnatin jihar Sokoto ta raba babura da keke napep ga 'yan achaɓar jihar a bisa farashi mai rahusa.
Gwamnan jihar wato Ahmed Aliyu ya bayyana cewa sun yi hakan ne domin sauƙaƙawa al'ummar jihar harkokin zirga-zirgarsu na yau da kullum.
Asali: Legit.ng