Sokoto: Sakataren Gwamnati Ya Shiga Jarabawa, 'Yarsa da Jikoki 3 Sun Rasu Lokaci Ɗaya

Sokoto: Sakataren Gwamnati Ya Shiga Jarabawa, 'Yarsa da Jikoki 3 Sun Rasu Lokaci Ɗaya

  • Ɗiyar sakataren gwamnatin jihar Sakkwato, Alhaji Muhammadu Bello da ƴaƴanta guda uku sun rasu a wata gobara da ta afku da tsakar dare
  • An ruwaito cewa gobarar ta kama ne a gidan babban sakataren ma'aikatar wasanni da ci gaban matasa, wanda shi ne mijin marigayiyar
  • Mataimakin gwamna da wasu ƴan majalisar zartarwa na jihar Sakkwato sun nufi garin Sifawa domin halartar jana'iza da kuma yin ta'aziyya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Sokoto - Sakataren Gwamnatin Jihar Sakkwato, Alhaji Muhammadu Bello Sifawa, ya rasa ‘yarsa da jikoki uku a wata mummunan gobara da ta faru a gidansu.

Ɗiyar sakataren gwamnatin da ƴaƴanta guda uku sun rasu a gobarar da ta tashi a gidanta da sanyin safiyar ranar Litinin, 6 ga watan Janairu, 2025.

Alhaji Muhammad Bello.
Diyar sakataren gwamnatin Sakkwato da yayanta sun rasu a wata gobara da ta kama da tsakar dare Hoto: Abu Chaji Milgoma
Asali: Facebook

Jaridar Vanguard ta tattaro cewa mamaciyar ta kasance matar babban sakataren ma’aikatar wasanni da ci gaban matasa ta jihar Sakkwato, Alhaji Muhammadu Yusuf Bello.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Sokoto ta fadi abin da za ta yi wa wadanda gobarar kasuwar Kara ta shafa

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sakataren gwamnatin Sokoto ya yi rashi

Gobarar ta barke ne da tsakar dare lokacin da duka iyalan suke barci, kuma rahotanni sun tabbatar da cewa mijin ɗiyar SSG ne kadai ya tsira daga wannan ibtila'i.

Har yanzu ba a gano musabbabin gobarar ba, wadda sai da jami’an kwana-kwana na jihar Sakkwato suka shafe awanni suna fafutukar kashe wutar kafin su samu nasara.

Wannan mummunan lamari ya girgiza al’umma da dama, musamman ma makusantan marigayiyar da iyalanta.

An shirya jana'iza a garin Sifawa

Bayanai sun nuna cewa an shirya jana'izar marigayiyar da ƴaƴanta uku yau a Masallacin Sheikh Shehu Usmanu Danfodiyo da ke garin Sifawa.

Za a yi jana'izar a gidansu Sakataren Gwamnatin Sakkwato watau mahaifin mamaciyar da ke garin Sifawa yau Litinin.

Gwamnatin Sakkwato ta tura wakilai wurin jana'iza

A halin yanzu mataimakin gwamnan jihar Sakkwato, Injiniya Idris Mohammed Gobir, tare da wasu ƴan majalisar zartarwa sun nufin garin Sifatawa don halartar jana'iza.

Kara karanta wannan

Mummunar gobara ta tashi a fitacciyar kasuwa, an samu asarar dukiya mai yawa

Haka zalika manyan jigogin jam’iyyar APC, abokan arziki, da masoya sun fara cika Sifawa domin halartar jana’izar da kuma mika ta’aziyya ga iyalan SSG.

Wannan al’amari ya kasance abin alhini da jimami ga ɗaukacin al’ummar Sifawa da ma sauran sassan jihar baki ɗaya, rahoton Daily Post.

Duk da cewa an yi kokarin gano dalilin barkewar gobarar, har yanzu ana ci gaba da bincike domin gano musabbabin wannan mummunan lamari.

Sakkwatawa sun yi alhinin wannan rashi

Al’ummar jihar Sakkwato sun bayyana wannan bala’i a matsayin wata babbar jarabta da ke bukatar hakuri da addu’a ga wadanda abin ya shafa.

A yayin da ake cikin wannan lokaci na jimami, mutane da dama sun bayyana alhinin su tare da rokon Allah ya jikan mamatan, ya ba su Aljannar Firdausi, kuma ya ba iyalansu hakuri da juriya.

Gobara ta tashi a kasuwar Kara

A wani rahoton, kun ji cewa gobara ta laƙume muhimman kayayyakin a kasuwar Kara da ke jihar Sakkwato a Arewa maso Yammacin Najeriya.

Kara karanta wannan

Tinubu na ganin sabuwar matsala daga Arewa, dattawa sun ƙi yarda da gyaran haraji

Rahotanni sun bayyana cewa gobatar ta babbake shagunan ƴan kasuwa da dama, sai dai jami'an hukumar bayar da agaji sun ba da tabbacin tallafa masu.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262