Bayar da Rance ga Talaka da Wasu Muhimman Abubuwa 9 da Tinubu Zai Aiwatar a 2025

Bayar da Rance ga Talaka da Wasu Muhimman Abubuwa 9 da Tinubu Zai Aiwatar a 2025

  • Gwamnatin Bola Tinubu za ta kaddamar da kamfanin samar da bashi na kasa a 2025 domin ba da rancen kudi ga 'yan Najeriya
  • Shirin Green Imperative zai samar da kayan aikin noma na zamani tare da ba da horo ga manoma a kananan hukumomi 774
  • Wadannan na daga cikin wasu muhimman shirye-shirye 10 da ake sa ran gwamnatin Tinubu za ta aiwatar a wannan shekarar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - A yayin da muka shiga shekarar 2025, yana da muhimmanci mu yi waiwaye kan manufofin da za su tsare-tsaren gwamnati da ake sa ran aiwatarwa.

Rahoto ya nuna cewa, shugaban kasa Bola Tinubu zai aiwatar da muhimman ayyuka da kaddamar da sababbin shirye shirye a shekarar 2025.

Cibiyar watsa labarai na Tinubu ta yi bayanin shirye shirye 10 da za a aiwatar a 2025
Shirye-shirye 10 da ake tsammanin Shugaba Bola Tinubu ai aiwatar a shekarar 2025. Hoto: @PBATMediaCentre
Asali: Facebook

Wani rahoto da cibiyar watsa labarai ta Shugaba Bola Tinubu ta fitar a shafinta na X, ya lissafa abubuwa 10 da Tinubu zai aiwatar a 2025.

Kara karanta wannan

Farfesoshin Jami’ar ABU Zaria sun fito da illolin da ke cikin kudirin gyaran haraji

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

1. Taron matasa na kasa

Ana sa ran fara taron matasa na kasa a farkon zangon shekarar 2025 domin karfafa hadin kai tsakanin matasa da shugabanni.

Taron zai tabbatar da kudirin gwamnati na saka matasa a cikin harkokin gwamnati da kuma saka hannun jari a matsayin masu gina kasa.

Ma’aikatar matasa za ta sanar da yadda za a fitar da wakilai daga dukkanin jihohi domin halartar taron nan ba da jimawa ba.

2. Kamfanin tabbatar da bashi na kasa

Ana sa ran gwamnatin Bola Tinubu za ta kaddamar da kamfanin tabbatar da bashi na kasa kafin karshen zangon shekarar 2025.

Wannan zai taimaka wajen samun damar ba da bashi ga ‘yan kasa da tallafawa bangarori masu muhimmanci na tattalin arziki.

3. Aiwatar da dokokin gyaran haraji

Ana sa ran majalisar tarayya za ta amince da kudurorin sake fasalin haraji da ake tattaunawa a kansu a halin yanzu a cikin watanni masu zuwa.

Kara karanta wannan

Amarya ta hada baki da tsohon saurayinta sun saka guba a abincin ango

Kudurorin za su karfafa tattara haraji, su gyara tattalin arziki, su rage talauci, hauhawar farashi, rashin aiki da kuma bunkasa saukin gudanar da kasuwanci.

4. Ba da rancen kudi (Kashi na 2)

Ana sa ran cigaba da shirin ba da rancen kudi na gwamnati, inda al'umma za su fara amfana daga wannan shiri mai muhimmanci.

Matakin farko ya baiwa dubban ma’aikatan gwamnati dama; yanzu ana fadada shi zuwa ga al’umma baki daya don bunkasa rayuwar jama’a.

5. Kaddamar da muhimman gine-gine

Ana sa ran kaddamar da wasu muhimman ayyukan gine-gine a 2025, ciki har da:

  • Hanyar Lagos-Calabar (aikin farko)
  • Tashoshin motoci 3 a Abuja
  • Biranen "Renewed Hope Cities"
  • Bututun gas na AKK
  • Masana’antar mai ta Kaduna
  • Aikin wutar lantarki na Maiduguri (MEPP)
  • Shirin "Presidential Power Initiative" (PPI)
  • Wutar lantarki ta Kudendan
  • Tashar wutar lantarki mai karfin 375MW ta Egbema

6. Shirin noma na SAP/GI

Shirin noma na SAP/GI na sarrafa kayan noma zai inganta samar da abinci a manyan matakai tare da kafa wuraren gyara amfanin noma a jihohi daban-daban.

Kara karanta wannan

Tinubu: Kalaman Peter Obi sun yi wa APC zafi, ta zarge shi da son tunzura jama'a

Shirin Green Imperative zai baiwa manoma a matakin karkara kayan aikin zamani, horo, da cibiyoyi a cikin kananan hukumomi 774 na Najeriya.

7. Aiwatar da 'yancin kananan hukumomi

Ana sa gwammatin Bola Tinubu za ta aiwatar da hukuncin kotun koli game da ‘yancin kananan hukumomi a wannan shekara.

Hakan zai bai wa gwamnatin tarayya damar aikawa kananan hukumomi kasafi kai tsaye ba tare da shiga tsakani daga jihohi ba.

8. Shirin kiwon dabbobi na kasa

Bayan kafa ma’aikatar dabbobi, ana sa ran fara shirin kiwon dabbobi na kasa domin bunkasa tattalin arziki da rage rikicin makiyaya da manoma.

Arewacin Najeriya, wanda ke da mahimmanci a kiwon dabbobi, zai taka rawa wajen kawo sauyi mai amfani ga tattalin arzikin kasa.

9. Sabon katin shaidar zama dan kasa

Ana sa ran kaddamar da sabon katin AFRIGO wanda hukumar shaidar zama dan kasa ta tsara a shekarar nan.

Katin zai taimaka wajen karfafa shigar kudi, bai wa ‘yan kasa damar samun ayyukan gwamnati, da dawo da kwarin gwiwa kan tsarin shaidar dan kasa.

Kara karanta wannan

Muhimman abubuwa 3 da 'yan Najeriya za su so ganin karshensu a 2025

10. Shirin garuruwan 'Renewed Hope'

Za a kafa garuruwan "Renewed Hope Creative Villages" a kowace jiha domin bunkasa masana’antar kere-kere da kuma kiyaye wuraren tarihi.

Shirin zai hade tare da gwamnatocin jihohi domin mayar da wuraren tarihi zuwa cibiyoyin kere-kere, da kuma samar da ayyuka da bunkasa tattalin arziki.

Tinubu zai kafa sabon kamfani a 2025

A wani labarin, mun ruwaito cewa shugaba Bola Tinubu ya ce gwamnatin tarayya na da kudurin saukaka rayuwar jama’a a shekarar 2025

Tinubu zai kafa kamfanin da zai kawo sauki ga talaka wanda zai tallafawa matasa da mata, karkashin hadin gwiwa da BOI, NSIA da Ma’aikatar Kudi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.