Gwamna Abba Ya Rantsar da Sababbin Kwamishinoni, Ya ba Su Muhimmiyar Shawara

Gwamna Abba Ya Rantsar da Sababbin Kwamishinoni, Ya ba Su Muhimmiyar Shawara

  • Sababbin kwamishinoni da masu ba da shawara na musamman da aka naɗa a jihar Kano sun kama rantsuwar aiki
  • Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf ya rantsar da sababbin masu muƙaman ne a gidan gwamnati a ranar Litinin, 6 ga watan Janairun 2025
  • Abba Kabir Yusuf ya buƙaci masu muƙaman da masu maida hankali wajen sauke nauyin da aka ɗora musu yadda ya kamata

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Kano - Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya rantsar da sabbabin kwamishinoni da masu ba da shawara na musamman da ya naɗa a gwamnatinsa.

Gwamna Abba Kabir Yusuf ya yi kira ga sababbin kwamishinoni da masu ba da shawarar, da su haɗa hannu da hukumomin ƙasa da mutanen da suke wakilta wajen gudanar da ayyukansu.

Gwamna Abba ya rantsar da kwamishinoni
Gwamna Abba ya rantsar da kwamishinoni da masu ba da shawara na musamman Hoto: @babarh
Asali: Twitter

Abba Kabir ya rantsar da sabbabin kwamishinoni

Kara karanta wannan

Rikici ya ɓarke tsakanin gwamna a Arewa da mai martaba Sarki? Bayanai sun fito

Jaridar Leadership ta rahoto cewa Gwamna Abba Kabir Yusuf ya yi wannan kiran ne a yayin bikin rantsar da sababbin kwamishinonin a ranar Litinin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamna Abba Kabir Yusuf, ya rantsar da sababbin kwamishinoni bakwai, masu ba da shawara 13, da manyan sakatarori guda shida a wani biki na musamman da aka gudanar a gidan gwamnati da ke Kano.

Wannan naɗi na daga cikin ƙoƙarin gwamnatin jihar na tabbatar da ingantaccen shugabanci da isar da manufofi masu ma’ana ga al’ummar Kano.

Sababbin kwamishinonin da aka naɗa sun haɗa da Shehu Wada Shagagi, Ismail Aliyu, Gaddafi Shehu, Dahiru Hashim, Abdulkadir Abdulsalam, Ibrahim Waiya da Nura Ma’aji.

Haka zalika, Antoni Janar kuma kwamishinan shari’a na jihar, Haruna Isa Dederi, ne ya jagoranci rantsar da waɗannan sababbin masu rike da muƙamai a hukumance.

Wace shawara Gwamna Abba ya ba da?

A yayin bikin rantsuwar, Gwamna Abba Kabir Yusuf ya yi kira ga sababbin kwamishinoni da masu muƙamai da aka naɗa da su sauke nauyin da ke kansu bisa gaskiya, adalci, da kishin ƙasa.

Kara karanta wannan

Kano: Ƴan Kwankwasiyya sun tashi da nauyi, Gwamna Abba ya ba su miliyoyin Naira

Ya jaddada cewa, aikin haɗin gwiwa da haɗa kai tsakanin dukkanin ɓangarorin gwamnati da al’umma yana da matuƙar muhimmanci wajen cimma burin ci gaban jihar Kano.

Gwamnan ya bayyana cewa gwamnatinsa ta dukufa wajen aiwatar da tsare-tsaren da za su inganta rayuwar al’ummar Kano, yana mai cewa nasarorin da ake fatan cimmawa za su dogara ne kan irin jajircewar da waɗanda aka naɗa za su nuna.

Ya kuma gargaɗe su da su tabbatar da cewa ayyukansu sun yi daidai da muradun al’umma da buƙatun jihar.

Gwamna Abba ya yabawa majalisar Kano

Bugu da ƙari, Gwamna Abba Kabir Yusuf ya yi godiya ta musamman ga majalisar dokokin jihar Kano ƙarƙashin jagorancin Jibril Isma’il Falgore.

Ya yaba musu kan jajircewa da haɗin kan da suke bai wa gwamnatinsa, wanda ya ce shi ne ginshiƙin nasarorin da aka samu a jihar.

Gwamna Abba ya ba da muƙamai

A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya raba manyan sababbin muƙamai guda biyar a gwamnatinsa.

Kara karanta wannan

Kwamishinan Kano ya yi murabus bayan dakatar da shi daga NNPP

Gwamna Abba ya naɗa masu ba da shawara na musamman guda biyar, inda ya bayyana cewa naɗin na su zai fara aiki ne nan take.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng