Taraba: Malaman Musulunci Sun Yi wa Gwamna Gata, An Sauke Masa Alkur'ani

Taraba: Malaman Musulunci Sun Yi wa Gwamna Gata, An Sauke Masa Alkur'ani

  • A ranar Asabar 4 ga watan Janairun 2024 aka gudanar da addu'o'i na musamman ga Gwamna Agbu Kefas da jihar Taraba
  • An gudanar da addu'o'in ne a Masallacin Juma'a na Saurara da ke birnin Jalingo domin taimakawa gwamnan samun nasarori a mulkinsa
  • Mataimakin gwamnan a bangaren harkokin addinin Musulunci, Hon. Hussaini Ismail shi ya tabbatar da haka ga wakilin Legit Hausa

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jalingo, Taraba - Al'ummar Musulmi sun gudanar da addu'o'i na musamman ga Gwamna Agbu Kefas na jihar Taraba.

An gudanar da addu'o'in ne a ranar Asabar 4 ga Janairun 2025 domin Gwamna Kefas da kuma ci gaban jihar Taraba gaba daya.

An gudanar da addu'o'i da saukar Alkur'ani ga Gwamnan Taraba
Manyan malaman Musulunci sun yi addu'o'i ga Gwamna Agbu Kefas na Taraba. Hoto: Hussaini Ismail.
Asali: Facebook

Taraba: An sauke Alkur'ani ga Gwamna Kefas

Hadimin gwamnan a bangaren harkokin addinin Musulunci, Alhaji Hussaini Ismail shi ya bayyana haka ga wakilin Legit Hausa a jiya Lahadi 5 ga watan Janairun 2025.

Kara karanta wannan

Gwamna ya dakatar da sarki da majalisarsa bayan korafin jama'a

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hadimin gwamnan ya ce sun taru a masallacin Juma'a na Saurara ne da ke birnin Jalingo domin addu'o'in zaman lafiya ga gwamnan da jihar.

Hon. Ismail ya fadawa Legit Hausa cewa manyan malaman Musulunci da dama ne kuma ɓangarori daban-daban suka halarci taron addu'o'in da kuma saukar Alkur'ani.

Musabbabin addu'o'i ga Gwamna Kefas

"Mun taru a nan domin yin addu'o'in musamman ga mai girma Gwamna Agbu Kefas da jihar Taraba gaba daya."
"Wannan taron ya gudana a Masallacin Juma’a na Saurara da ke Jalingo, inda manyan limamai da malaman addinin Musulunci suka halarta daga sassa daban-daban na jihar."
"A cikin addu'o'insu, malaman sun roki Allah ya ci gaba da jagorantar Gwamna Kefas, ya ba shi lafiya mai kyau da nasara mai dorewa a aikinsa."

- Alhaji Hussaini Ismail

Hussaini Ismail

Hadimin gwamna ya fadi shirin Kefas a Taraba

A jawabinsa, Hon. Ismail ya tabbatar wa da mahalarta taron cewa Gwamna Agbu Kefas yana da cikakken kudiri na ci gaba da gina Taraba mai nagarta.

Kara karanta wannan

Rarara ya tara malamai 1,000 domin neman tsari daga sharrin bokayen Nijar, an yi addu'oi

Ya yi kira ga daukacin al’umma, musamman ‘yan’uwa Musulmai, da su ci gaba da bayar da goyon baya ga gwamnati domin samun kyakkyawar makoma ga jihar.

Hon. ya ce wannan addu’a ta musamman ta nuna karfin dangantaka tsakanin al’ummar Musulmai da gwamnatin Taraba, da kuma sadaukarwarsu wajen tabbatar da zaman lafiya, hadin kai, da ci gaba a jihar.

Malaman addinin Musulunci daga bisani sun jinjina wa Gwamna Agbu Kefas kan kokarinsa na gina Taraba mai nagarta ga kowa da kowa.

Rarara ya jagoranci addu'o'i ga Najeriya

A baya, mun ba ku labarin cewa ana ta hasashen alaka na kara tsami tsakanin Najeriya da Nijar, Dauda Kahutu Rarara ya jagoranci addu'o'i na musamman a Katsina.

Mawakin na daga cikin wadanda suke sukar shugaban soji na kasar Nijar, Janar Abdourahamane Tchiani game da zarginsa kan Najeriya.

Rarara ya dauki nauyin malamai akalla guda 1,000 saboda yin addu'o'i da saukar Alkur'ani domin kare Najeriya.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.