'Talaka Ya Samu Abinci': Sarakuna Sun Haskawa Tinubu Hanyar Gyara Tattalin Arziki
- Sarakunan gargajiya sun yi kira ga gwamnatin Bola Tinubu da ta magance matsalolin tattalin arziki da na karancin abinci
- Iyayen kasar sun nuna alhini kan rashin rayukan da aka yi a turereniyar karbar tallafin abinci da aka yi a Abuja, Anambra, da Oyo
- Sarakunan sun kuma yi hasashen kyakkyawar makoma ga Najeriya a shekarar 2025 tare da kira ga hadin kai da zaman lafiya
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Oyoyo - Sarakunan gargajiya sun bukaci gwamnatin tarayya ta gaggauta magance matsalar karancin abinci da wahalar tattalin arziki.
Sarakunan daga Kudancin Najeriya sun ce kasar nan za ta samu kyakkyawar makoma a shekarar 2025, duk da kalubalen da ake fuskanta.
Turereniya: Sarakuna sun yi wa jihohi ta'aziya
Jaridar Vanguard ta rahoto iyayen kasar sun yi magana kan turereniyar da ta faru yayin raba tallafin abinci a wasu jihohi, wanda ya jawo asarar rayuka.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A cikin wata sanarwa daga majalisar sarakunan gargajiya ta Kudancin Najeriya, sun bayyana alhini kan abubuwan da suka faru.
Sarakunan sun mika ta’aziyya ga iyalan wadanda suka rasa rayukansu a turmutsutsun karbar tallafi da ya faru a Abuja, Anambra, da Oyo.
Sarakuna sun ba da shawara kan tarukan jama'a
Sarakunan sun bukaci gwamnati ta ci gaba da yin aiki tukuru don inganta tattalin arziki da rage wahalar rayuwa a tsakanin al’umma.
Sun kuma shawarci masu shirya taruka da su yi amfani da jami’an tsaro wajen tsara shirye-shiryensu don kauce wa cunkoso, inji rahoton Daily Trust.
“Dole ne a tabbatar an dauki matakai na kare rayuka da lafiyar mahalarta taro wanda zai fara daga lokacin da ake shirin gudanar da irin wannan taron."
- A cewar sarakunan.
"A magance matsalar tattali" - Sarakuna
Sun kuma bukaci gwamnati, masu shirya taruka da hukumomin tsaro su dauki matakan kariya don kauce wa faruwa ire-iren wadannan abubuwan.
“Abin bakin ciki ne. Muna mika ta’aziyyarmu ga iyalan wadanda suka rasa rayukansu a turereniyar da ta faru a jihohin kasar nan.”
“Wadannan abubuwan sun kara nuna muhimmancin bukar da ke da akwai ta magance matsalolin tattalin arziki da ke addabar kasar.”
- A cewar sanarwar.
Hasashen sarakuna kan shekarar 2025
Sarakunan sun yi hasashen cewa Najeriya za ta samu ci gaba a shekarar 2025 ta hanyar koyon darasi daga kalubalen da ta fuskanta a 2024.
Sun yi imanin cewa kalubalen da kasar ta fuskanta kuma ta fita daga cikinsu a 2024 za su taimaka wajen magance matsalolin 2025.
Sun jaddada bukatar hadin kai tsakanin ‘yan Najeriya, ba tare da la’akari da bambance-bambancen addini ko kabilanci ba.
"Za a samu sauki a 2025" - Hasashen Fasto
A wani labarin, mun ruwaito cewa shugaban Cocin Freedom Apostolic Revival Fasto Samuel Adebayo Ojo, ya ce wahalhalun Najeriya za su kare nan gaba kadan.
Yayin taron shekara-shekara a Ori Oke Ogo kusa da Ibadan, malamin ya hango cewa 2025 za ta samu karuwar alheri da kwanciyar hankali a wannan shekarar.
Malamin ya bayyana wa dubunnan masu ibada cewa Ubangiji ya nuna masa cewa wahalhalun Najeriya za su ragu a shekarar 2025.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng