Rarara Ya Tabo Tsuliyar Dodo, An ba Shi Wa'adi Ya Janye Kalamansa kan Shugaban Nijar

Rarara Ya Tabo Tsuliyar Dodo, An ba Shi Wa'adi Ya Janye Kalamansa kan Shugaban Nijar

  • Ustaz Abubakar Salihu ya magantu kan kalaman Dauda Kahutu Rarara, wanda ya bukaci Janar Tchiani ya sauka daga mulkin Nijar
  • Malamin ya yi martani mai zafi, inda ya ba Rarara wa’adin mintuna 20 ya janye kalamansa kan shugaban kasar na Nijar
  • Ustaz Abubakar ya jaddada bukatar zaman lafiya da hadin kai tsakanin Najeriya da Nijar, yana Allah-wadai da kalaman Rarara

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Kaduna - Malamin addinin Musulunci, Ustaz Abubakar Salihu Zaria ya yi tsokaci kan takaddamar da ake yi game da shugaban Nijar, Janar Abdourahamane Tchiani.

Ustaz Abubakar ya yi martani mai zafi ga mawaki Dauda Kahutu Rarara, wanda ya ba Tchiani wa'adin kwana 20 ya mika mulkin Nijar ga farar hula.

Malamin addini, Ustaz Abubakar ya ba Rarara wa'adi ya janye kalamansa kan shugaban Nijar.
Ustaz Abubakar Zaria ya bukaci Rarara ya janye kalamansa kan shugaban kasar Nijar. Hoto: General Abdourahamane Tciani Officiel/Dauda Kahuta Rarara
Asali: Facebook

A cikin wani faifan bidiyo da Gen Sanusi ya wallafa a shafinsa na Facebook, an ji malamin na cewa "rashin hankali da jahilci" ya sa Rarara furta kalamansa.

Kara karanta wannan

Rarara ya tara malamai 1,000 domin neman tsari daga sharrin bokayen Nijar, an yi addu'oi

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Matashiya: Abin da mawaki Rarara ya ce

Tun da fari, Legit Hausa ta rahoto cewa mawaki Rarara, ya nuna bacin ransa kan gazawar sojoji na dawo da mulki ga fararen hula a Jamhuriyar Nijar.

A wata tattaunawa, Rarara ya zargi Janar Abdourahamane Tchiani da garkuwa da tsohon shugaba Bazoum da hana mutanen Nijar ‘yancin walwala a kasarsu.

Mawakin ya yi alkawarin amfani da basirarsa wajen yin wakokin wayar da kan jama’a game da illolin mulkin Janar Tchiani da tasirinsa akan al’ummar Nijar.

An ce Rarara ya ba Janar Tchiani wa'adin kwanaki 20 da ya gaggauta mika mulki ga farar hula ko ya fuskanci fushin jama'a.

Ustaz Abubakar ya yi wa Rarara martani

A kan wannan ne, Ustaz Abubakar ya dura kan Rarara, ya ba mawakin wa'adin mintuna 20 da ya janye kalaman da ya yi kan shugaban kasar Nijar.

A cikin bidiyon malamin addinin ya ce:

Kara karanta wannan

Janar Tchiani ya komawa bokaye yayin da kasar Nijar ke ‘yar tsama da Najeriya

"Ko kansilar unguwarku ka iya ba shi kwana 20 ka ce ya sauka ballantana shugaban wata kasa? To shi ma mun ba shi minti 20 ya gaggauta janye wannan maganar.
"Ba ya ce zai yi wakoki tara ba? To mu za mu ba shi ayoyi tara sau tara kuma sau 99. Mu idan jahili ya buga jahilci, mu kuma sau mu buga almajirci."

"Hadin kan Nijar da Najeriya muke so" - Abubakar

Malamin addinin ya jaddada cewa abin da ake bukata a yanzu shi ne dorewar zaman lafiya da hadin kai tsakanin Najeriya da Nijar, yana mai cewa:

"Fatanmu hadin kanmu ya dore. Allah kadai ya san 'yan Nijar da ke zaune a Najeriya, Allah ne kadai ya san 'yan Najeriya da ke zaune a Nijar."

Legit Hausa ta fahimci cewa wa'adin mintuna 20 da malamin ya debarwa mawakin tuni suka cika, kuma har yanzu ba a ji amsa daga Rarara ba.

Kara karanta wannan

Peter Obi ya ziyarci IBB, ya bayyana abubuwan da suka tattauna a kan Najeriya

Kalli bidiyon a kasa:

Rarara ya tara malamai 10,000 su yi addu'a

A wani labarin, mun ruwaito cewa mawakin siyasa, Dauda Kahutu Rarara ya tara malamai 1,000 domin yin addu'o'i kan shugaban Nijar.

An ce mawaki Rarara ya jagoranci taron addu'o'i a garin Kahutu, jihar Katsina, domin neman kariya daga sharrin bokayen Jamhuriyyar Nijar.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.