'Zargin Maita': Wasu Fusatattun Matasa Sun Bankawa Mutumi Wuta har Lahira

'Zargin Maita': Wasu Fusatattun Matasa Sun Bankawa Mutumi Wuta har Lahira

  • Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta kama mutane 17 da ake zargi da kashe wani mutumi a jihar Ebonyi, bisa zargin yana maita
  • An zargi Uromchi Okorocha, da zama silar mutuwar wasu mutane ta hanyar lashe kurwarsu, lamarin da ya jawo aka kona shi
  • Sufeto janar na ‘yan sanda ya yi Allah wadai da masu daukar doka a hannu, yana kira ga al’umma su rika kai rahoto ga hukumomi

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Ebonyi - Rundunar ‘yan sanda a jihar Ebonyi da ke Kudu maso Gabas ta kama mutane 17 da ake zargi da kona wani mutum bisa zargin maita.

Kakakin rundunar, Olumuyiwa Adejobi, ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa ranar Lahadi, inda ya ce lamarin ya faru a ranar 3 ga Janairu, 2025.

Yan sanda sun magantu yayin da wasu fusatattu suna kashe wani mutumi kan zargin maita a Ebonyi
'Yan sanda sun kama mutane 17 kan zargin bankawa wani mutumi wuta kan maita. Hoto: @PoliceNG
Asali: Twitter

An kashe dan Najeriya kan zargin maita

Kara karanta wannan

Karshen shekara: NDLEA ta tafka kwamushe a Legas da Kano, an kame fitaccen dan fim

Olumuyiwa ya ce an yi kisan ne a kauyen Enohia Itim da ke karamar hukumar Afikpo ta Arewa, kamar yadda Premium Times ta rahoto.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mista Olumuyiwa ya bayyana sunan wanda aka kashe da Uromchi Okorocha, sannan ya ce an kama mutane 17 a kauyen bisa zargin kashe shi.

Kakakin rundunar 'yan sandan ya ce matasa a kauyen sun zargi marigayin da kashe wasu mutane ta hanyar lashe kurwarsu.

Fusatattu sun kona wanda ake zargin

A cewar mai magana da yawun 'yan sandan :

"Mutanen sun taru suka kama marigayin, amma maimakon mikashi ga hukuma, sai suka dauki doka a hannunsu suka kashe shi.
"Rundunar ‘yan sanda ta Uwanna ta aike da tawagar ‘yan sanda zuwa wurin da lamarin ya faru don ceton marigayin, amma aka tarar har an kashe shi."

Adejobi ya kara da cewa an kone Okorocha kafin zuwan jami’an tsaro, duk da kokarin da ‘yan sanda suka yi.

Kara karanta wannan

'Ku dage da addu'a;" Malamin addini ya hango abin da zai faru da Najeriya a 2025

Sufetan 'yan sanda ya yi Allah-wadai

Sufeto Janar na ‘yan sandan Najeriya, Kayode Egbetokun, ya la’anci kisan gilla da ake yi ba tare da bin doka ba.

Ya yi kira ga ‘yan Najeriya da su guji daukar doka a hannunsu kuma su kai rahoton duk wani zargi ga hukuma mafi kusa.

IGP Egbetokun ya ce daga aikin ‘yan sanda akwai tabbatar da cewa an kama tare da hukunta masu aikata laifuffuka.

'Yan sanda sun nemi hadin kan jama'a

Egbetokun ya sake jaddada aniyar rundunar wajen tabbatar da tsaron al’umma da bin doka wajen samar da adalci ga wadanda abin ya shafa.

Ya bukaci jama’a da su hada kai da jami’an tsaro, su bayar da bayani kan duk wani abu da zai taimaka wajen rage aikata laifuka.

Kisan da ake dangantawa da maitar ya zama matsala mai tsanani a yankin kudancin Najeriya, inda ake yawan samun ire-iren wadannan ayyuka na maita.

Kara karanta wannan

Yadda aka tattaro wasu barayi da 'yan bola jari masu sayen kayan sata

Mahaifi ya bankawa 'ya'yansa wuta

A wani labarin, mun ruwaito cewa rundunar ‘yan sandan Filato ta ce wani mutum mai suna Nyam Choji ya bankawa ‘ya’yansa biyu wuta bisa zargin maita a kauyen Shen.

Yaran, Godsgift Nyam mai shekaru 11 da Mary Nyam mai shekaru 5, an kwantar dasu a asibitin kwararru na Jos don kula da konewar da suka yi.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.