Kwamishinan Kano Ya Yi Murabus bayan Dakatar da Shi daga NNPP
- Kwamishinan Ma'aikatar Kula da Ayyukan Gwamnatin Kano, Muhammad Diggol ya ajiye mukaminsa a gwamnatin Abba
- A cikin wata sanarwa da Sanusi Bature ya fitar, Gwamna Abba Kabir Yusuf ya amince da murabus din da Diggol ya yi
- Ya gode wa Injiniya Diggol bisa gudunmawar da ya ba gwamnatinsa da jajircewarsa wajen gudanar da aiki
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kano - Kwamishinan Ma’aikatar Kula da Ayyukan Gwamnati a Jihar Kano, Injiniya Muhammad Diggol, ya yi murabus daga mukaminsa. Ya ajiye aikin ne ana dab da rantsar da sababbin kwamishinonin da majalisar dokokin Kano ta amince da su bayan Gwamna Abba Kabir Yusuf ya aika da sunayensu.
A sakon da Daraktan Yada Labaran Gwamnatin Kano, Sanusi Bature Dawakin ya a wallafa a shafinsa na Facebook, Gwamna Abba Kabir Yusuf ya amince da murabus ɗin Injiniya Diggol.
Dalilin murabus na kwamishinan Kano
Jaridar Vanguard ta wallafa cewa duk da ba a bayyana dalilin yin murabus ɗin Injiniya Diggol ba, lamarin ya faru ne jim kaɗan bayan sauyin da aka yi wa majalisar zartarwa ta jihar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sannan kafin wannan lokaci, NNPP ta dakatar da Diggol tare da tsohon Sakataren Gwamnatin Jihar, Dr. Abdullahi Baffa Bichi bisa zargin rashin biyayya ga shugabancin jam’iyyar.
Fatan gwamna Abba ga tsohon kwamishinan Kano
Gwamna Abba Kabir Yusuf ya jinjinawa Injiniya Muhammad Diggol bisa gudunmawar da ya bayar a cikin wa’adin mulkinsa, tare da yi masa fatan alheri a ayyukansa da ya sa a gaba.
Sanarwar da Sanusi Bature ya fitar ta ce;
“Gwamna Yusuf ya gode wa Injiniya Muhammad Diggol bisa jajircewarsa, sadaukarwa da kuma kwarewarsa a cikin lokacin da ya yi yana aiki a matsayin ɗan majalisar zartarwa ta jihar.
“Gwamnan ya kuma yi wa Injiniya Diggol fatan alheri a dukkanin ayyukan da zai runguma nan gaba,”
Makomar tsohon kwamishinan Kano
Yanzu haka, ana ci gaba da fargabar irin matakin da Injiniya Muhammad Diggol zai ɗauka a siyasa, ganin cewa yana daga cikin waɗanda suka taka rawar gani a cikin gwamnatin Gwamna Yusuf. Ana hasashen Diggol na iya komawa cikin NNPP idan aka sasanta rikicin da ke tsakaninsa da shugabancin jam’iyyar, ko kuma ya kalli wata sabuwar dama ta siyasa.
Gwamnan Kano zai nada sababbin kwamishinoni
A baya, mun ruwaito cewa Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, ya amince da wasu nade-nade domin ƙarfafa gudanarwar gwamnatinsa, tare da sanya ranar Litinin, 6 Janairu, 2025 don nadinsu.
Daraktan Kamar na yada labaran Gwamnan, Sanusi Bature Dawakin Tofa, ya bayyana hakan a ranar Lahadi, 5 yana mai cewa matakin zai taimaka wajen cimma manufar gwamnati.
Asali: Legit.ng