Rarara Ya Tara Malamai 1,000 domin Neman Tsari daga Sharrin Bokayen Nijar, an Yi Addu'oi
- Yayin da ake hasashen alaka na kara tsami tsakanin Najeriya da Nijar, Dauda Kahutu Rarara ya jagoranci addu'o'i na musamman a Katsina
- Mawakin na daga cikin wadanda suke sukar shugaban soji na kasar Nijar, Janar Abdourahamane Tchiani game da zarginsa kan Najeriya
- Rarara ya dauki nauyin malamai akalla guda 1,000 domin yin addu'o'i da saukar Alkur'ani domin kare Najeriya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Danja, Katsina - Mawakin siyasa a Najeriya, Dauda Kahutu Rarara ya jagoranci gudanar da addu'o'i ga Najeriya.
Mawaki Rarara ya dauki nauyin akalla malamai guda 1,000 domin addu'o'i da saukar Alkur'ani domin kare kasar daga sharrin bokayen Nijar.
Bokayen Nijar sun shirya kare kasarsu daga makarkashiya
Mataimakin mawakin a bangaren yada labarai, Rabiu Garba Gaya shi ya tabbatar da haka a shafinsa na Facebook a yau Lahadi 5 ga watan Janairun 2024.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wannan na zuwa ne bayan kungiyar bokayen Nijar sun shirya tura aljanu domin kare kasarsu daga sharrin wasu ƙasashe.
Malaman tsibbun za su bukaci rundunonin aljannunsu su ga bayan masu shiryawa Nijar makarkashiya.
Ana zargin cewa Janar Abdurrahmane Tchiani wanda ya kifar da gwamnatin farar hula ta Mohamed Bazoum ya yi zama da kungiyoyin bokaye a Nijar.
Rarara ya biya malamai 1,000 domin yin addu'o'i
Garba Gaya ya ce mai gidan nasa ya yi hakan ne domin neman kariya daga sharrin shugaban kasar Nijar.
An gudanar da addu'o'in ne a garin Kahutu da ke karamar hukumar Danja a jihar Katsina da ke Arewacin Najeriya.
Rarara ya soki shugaban Nijar, Tchiani
Kun ji cewa mawakin siyasa, Dauda Kahutu Rarara ya yi fatali da zarge-zargen da shugabanni Nijar, Abdourahamane Tchiani ke yi kan Najeriya.
Rarara ya ce wadannan zarge-zarge soki-burutsu ne kawai inda ya ce babu wanda ke cin dunduniyar Nijar kamar Tchiani.
Wannan na zuwa ne bayan Janar Tchiani ya zargi Najeriya da hada baki da Faransa domin kawo tsaiko a mulkinsa da kuma daukar nauyin Lakurawa.
Asali: Legit.ng