Sojojin Saman Najeriya Sun Saki Bama Bamai a Neja, An Halaka 'Yan Ta'adda da Dama
- Rundunar sojojin saman Najeriya ta saki bama baman kan sansanonin 'yan ta'adda a dajin Alawa da ke yankin Shiroro, jihar Neja
- Rahoto ya ce 'yan ta'adda irinsu Saddiku, Umar Taraba da Kabiru Doctor na cikin wadanda ke gudanar da ta'addanci a yankin
- An ce harin da sojojin ya yi nasarar lalata kadarori, makamai da motocin 'yan ta'addan kuma an halaka miyagun da dama
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Neja - Rundunar sojin sama ta Najeriya (NAF) ta kai hare-haren sama kan 'yan ta'adda a dajin Alawa da ke yankin Shiroro, a jihar Neja.
Hare-haren ta sama sun yi sanadin kashe 'yan ta'adda da dama tare da kuma lalata kadarorinsu da rage karfinsu sosai a yanki.
Saddiku, Umar Taraba da Kabiru DoctorSojoji sun farmaki 'yan ta'adda a Neja
A rahoton da Zagazola Makama ya wallafa a shafinsa na X, an ji cewa daga cikin shugabannin JAS da aka yi niyyar kashewa a harin akwai Saddiku, Umar Taraba da Kabiru Doctor.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sojojin saman Najeriya sun yi imanin cewa wadannan hatsabiban 'yan ta'addan na gudanar da ayyukansu ne a wadannan yankuna.
Wannan hari da sojojin suka kai ya kasance wani bangare na kokarin ci gaba da karya lagon mahara tare da tabbatar da zaman lafiya a yankin Neja.
Neja - Sojoji sun yiwa 'yan ta'adda barna
Zagazola Makama, wanda ya kasance mai sharhi kan lamuran tsaro a yankin tafkin Chadi ya rahoto cewa an lalata makamai, babura da motocin 'yan ta'addan a yayin harin.
Bama baman da sojojin saman Najeriya suka saki sun haifar da babbar asara ga 'yan ta'adda, lamarin da ya tilasta musu tserewa daga dajin Alawa.
Rahotanni sun ce maharan da suka tsere sun fara komawa Birnin Gwari da ke a jihar Kaduna, yankin da aka sani da tarihin rikice-rikice.
Sojoji za su ci gaba da kai hare-hare
Rahoton ya kuma bayyana cewa dajin Alawa na da dogon tarihi na zama mafakar wasu tsageru da ke aikata ta'addanci.
Bayanan asiri sun kuma nuna cewa Birnin Gwari, tsohuwar mafakar Ansaru da ke kokarin kafa kalifanci na iya zama sabon sansanin mahara.
An ce sojoji za su ci gaba da kai hare-hare a Birnin Gwari don tabbatar da ci gaba da kakkabe 'yan ta'adda da hana yaduwar su a yankin.
Wannan aiki ya nuna jajircewar NAF wajen yakar ta’addanci tare da kare rayuka da dukiyoyin jama’a daga barazanar 'yan ta'adda.
Neja: DSS ta tura tseguru zuwa barzahu
A wani labarin, mun ruwaito cewa jami’an DSS sun kashe ƴan bindiga uku a Dogon Dawa, Mariga, Jihar Neja, yayin wata musayar wuta a ranar Juma’a.
Wasu ƴan bindiga da dama sun tsere da raunukan harbin bindiga, yayin da jami’an DSS suka ƙwato bindigogi AK-47 uku da babura uku.
Majiyoyi sun bayyana cewa harin ya biyo bayan tattara bayanan sirri na tsawon makonni da nazarin sadarwa tsakanin ƴan bindigan da DSS.
Asali: Legit.ng