Tinubu na Ganin Sabuwar Matsala daga Arewa, Dattawa Sun Ƙi Yarda da Gyaran Haraji
- Kungiyar dattawan Arewa (NEF) ta bukaci Shugaban Bola Tinubu da ya janye kudurorin gyaran haraji da ta gabatarwa majalisa
- NEF ta zargi gwamnatin Tinubu da yin kama-karya wajen tsara kudurorin da kuma hana mutane furta ra'ayoyinsu kan dokokin
- Dattawan Arewa sun bukaci Tinubu ya dakatar da batun karin harajin VAT har sai an tabbatar da farfadowar tattalin arziki
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Kungiyar dattawan Arewa (NEF) ta nemi gwamnati ta dakatar da aiwatar da kudirorin sake fasalin haraji da aka gabatar.
Kungiyar ta zargi gwamnati da rashin tuntubar kwararru da al’ummar kasa kafin tsara dokar.
Dattawan Arewa sun sake magana kan haraji
Jagoran kungiyar, A.M. Al-Amin Daggash, ya ce wannan mataki zai yi illa ga yankin Arewa da Najeriya baki ɗaya a cewar rahoton The Guardian.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Al-amin Daggash ya jaddada cewa tattaunawar bai kamata ta zama tsakanin Arewa da Kudu kawai ba, amma ga dukkanin 'yan Najeriya.
Ya bayyana cewa gudummawar da ake samu daga yankuna daban-daban na ƙasar suna taimaka wa wajen gyaran dokar harajin.
Kungiyar NEF ta zargi gwamnati da yin kama-karya wajen ƙuntata ra'ayoyin masu sukar kudirorin haraji.
NEF ta zargi Tinubu da kuntatawa jama'a
Shugaban kungiyar dattawan Arewa ya bayyana takaicin yadda gwamnati ta toshe bakin jama’a wajen fadin ra’ayoyinsu.
"Abin tayar da hankali ne a irin wannan zamanin, ace an samu gwamnati da take tauye hakkin 'yan kasarta na furta ra'ayoyinsu kan kudurorinta.
- Al-Amin Daggash.
Ya yi Allah wadai da salon tilastawa jama’a su karbi abin da ya kira "matsananciyar doka," yana mai cewa:
"Tun bayan hawanta mulki, gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ta dauki matakan dakile muryar duk wani wanda zai fito ya kalubalanci manufofi da tsare-tsarenta."
Kungiyar ta bayyana cewa ba su adawa da gyare-gyare masu amfani, amma suna bukatar tsari mai cike da gaskiya da adalci.
Dattawan Arewa sun ba Tinubu shawarwari
Kungiyar NEF ta bayar da shawarar samar da tsare-tsare masu fayyace komai game da kudirorin, tare da wayar da kan jama’a.
Kungiyar ta jaddada cewa ya kamata gyare-gyaren haraji su dace da ƙa’idojin duniya da buƙatun al’umma.
Ta bukaci gwamnati ta dakatar da karin VAT don gujewa matsi kan rayuwar jama’a da karuwar hauhawar farashi.
NEF ta nemi a sake duba dokar tare da tattaunawa domin warware matsalolin da aka gano.
Ta jaddada cewa bukatar da ke da akwai na gwamnati ta bai wa duk ‘yan Najeriya damar fadin ra’ayoyinsu ba tare da tsangwama ba.
Haraji: Dattawan Arewa sun gargadi Tinubu
A wani labarin, mun ruwaito cewa, kungiyar dattawan Arewacin Najeriya (NEF) ta yi watsi da Dokar Gyaran Haraji, tana mai cewa an tsara ta ne da muguwar manufa.
NEF ta soki Shugaba Bola Tinubu kan rashin tuntubar masu ruwa da tsaki, ciki har da 'yan majalisar tattalin arziki, kafin shirya dokar gyaran harajin.
Asali: Legit.ng