Bikin Cika Shekara: Yadda Uwa Ta Shafe Kwanaki Tana Kirga Kudin da Baki Suka Watsawa 'Yarta

Bikin Cika Shekara: Yadda Uwa Ta Shafe Kwanaki Tana Kirga Kudin da Baki Suka Watsawa 'Yarta

  • Wata uwa ‘yar Najeriya ta wallafa bidiyo mai kayatarwa da ke nuna yawan kudin da baki suka watsa a wajen bikin cikar ‘yarta shekara guda
  • A cewarta, ita da wasu ‘yan uwanta sun shafe kusan kwanaki biyar suna kirga kudin, amma har yanzu ba su gama ba
  • Mutane a shafin TikTok da suka ga bidiyon sun yi addu’ar samun irin wannan arziki da kuma kasancewa tare da masu hannu da shuni

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wata uwa daga Najeriya ta jawo hankalin jama’a a shafukan sada zumunta bayan ta wallafa bidiyo mai nuna tarin kudin da baki suka watsa wa ‘yarta a ranar cikar shekararta ta farko.

Bidiyon ya nuna bikin da aka gudanar cikin walwala da alfahari, inda baki suka yi ta watsa kudi ga karamar yarinyar.

Yadda aka watsawa yarinya kudi
An watsa kudi a bikin cikar shekarar jaririya | Hoto: @chizaram/TikTok
Asali: TikTok

Mahaifiya ta nuna taron daki cike da kudi

Mahaifiyar, wacce ke amfani da sunan @chizaram a TikTok, ta wallafa bidiyon da ya nuna irin yadda baki suka yi ta watsa kudi har suka cika daki.

Kara karanta wannan

Kamfanonin sadarwa a Najeriya na son kara farashin kira da kashi 100

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cikin bidiyon, ta bayyana cewa:

"Har yanzu muna kirga kudi tsawon kwanaki biyar yanzu. Na gaji sosai. Ranar murnar cikar ‘yata shekara guda."

Masu amfani da TikTok sun yi martani

Masu amfani da kafar TikTok da suka ga bidiyon ba su boye mamakinsu ba, yayin da suka yabawa arzikin iyalin da kuma karimcin bakin.

Mutane da dama sun yi addu’a tare da fatan samun irin wannan nasara da kuma arziki.

Ga wasu daga cikin martanin masu amfani da TikTok:

@Zufrat ta ce:

"Ba zan ci gaba da kirge ba, zan rufe dakin ne kawai; duk lokacin da nake bukatar kudi, zan bude dakin in dauka."

@nzube001 ta ce:

"Ina iya shaida hakan, lokacin bikin aurena na gargajiya, Kaiiii, kirga kudi zai gajiyar da kai."

@Gloria ta ce:

"Dan Allah, ‘yan uwa, kawai ku taimake ni da wurin zama, don Allah."

@ODUMODU WHITE ya ce:

Kara karanta wannan

An ware biliyoyi domin yin hidima ga Akpabio, Barau da sauran shugaban majalisa

"Ya Allah, ka bani wannan irin matsalar, na yi alkawarin ba zan yi korafi ba."

@saintmelax ya tambaya:

"Ina mutane ke samun irin wannan kudi? Dan Allah, ina bukatar bayani a 2025."

@OmahJay ya ce:

"Zan kirga kudi ni kadai, ko da zai dauki kwanaki 365, babu matsala."

@CAKES/CATERER IN NNEWI/ANAMBRA ya rubuta:

"Ina Nnewi, dan Allah ina adireshi? Wannan irin matsalar ce nake so."

@lambertfavour418 ya tambaya:

"Idan kudin sun yi yawa haka, me ya sa ba ku sayi na’urar kirge ba?"

@Mayowa Olowonefa ya ce:

"Haka mutane za su taru su yi ta kirga kudina. Na tafi da wannan addu’a."

@Timmylee ta bayyana:

"Wannan irin aiki da matsalar nake so wa mijina. Ya Allah, ka albarkaci kokarin mijina da nawa ma."

@N̷a̷d̷i̷a̷ ta ce:

"Idan na gano inda ake samun irin wannan kudi ehhh, sai Allah ya cire hannuna."

@user8755963146678 ya ce:

Kara karanta wannan

Tinubu: Kalaman Peter Obi sun yi wa APC zafi, ta zarge shi da son tunzura jama'a

"Na yi karatun kirge kudi a jami’a. Don Allah, ku kira ni."

@𝓗𝓪𝓻𝓶𝓸𝓷𝔂 ta ce:

"Ya Allah, wannan irin matsalar ce kawai nake so a rayuwata. Ameen."

@Blessing Augustine611 ta ce:

"Wannan ita ce matsalar da nake so a rayuwata a 2025. Allah, ka kawo min ita."

@naijaboi ya ce:

"Mutane na son kudin su kasance cikin leda mai kyau (abin da bai dace ba). Ku dai kirga ku wuce kawai."

@lil_zina ta kara da cewa:

"Ya Ubangiji, ka bani irin wannan matsalar a cikin sunan Yesu. Wannan ita ce addu’ata a wannan shekara."

Ango da amarya sun kirga kudaden da aka watsa musu

A wani labarin, kun ji yadda wani ango da amaryarsa suka kirga kudaden da baki suka watsa musu a lokacin biki.

Wannan lamari ya dauki hankali, inda jama'a da yawa suka yi fadin albarkacin bakinsu kan abin da ya faru.

Ba sabon abu bane a yi biki a Najeriya sannan a watsa kudade, lamarin da ke daukar hankalin jami'an tsaro.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.