Murnar zagayowar ranar haihuwa: Dan Majalisa ya saya ma Uwargidarsa motar N75,000,000

Murnar zagayowar ranar haihuwa: Dan Majalisa ya saya ma Uwargidarsa motar N75,000,000

Shugaban masu rinjaye a majalisar wakilan Najeriya, Femi Gbajabiamila ya janyo ruwan dafa kansa bayan ya saya ma matarsa wata motar alfarma, kirar Marsandi G-Wagon da kudinsa ya kai naira miliyan saba’in da biyar, don murnar zagayowar ranar haihuwarta.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito Gbajabiamila ya baiwa Matar tasa, Yemisi, kyautar motar ne a ranar 27 ga watan Mayu, yayin bikin cikarta shekary 50, inda ya daura mata ‘ASSURANCE’ a lambar motar, wato tabbacin soyayya.

KU KARANTA: Yadda wasu matasa suka haƙo wata yarinya daga kabarinta suka datse mata kai a Adamawa

Murnar zagayowar ranar haihuwa: Dan Majalisa ya saya ma Uwargidarsa motar N75,000,000
Motar da Matar

Sai dai wannan biki bidiri da dan majalisar ya yi ya janyo cece kuce a hannun yan Najeriya, musamman a shafukan zumunta na yanar gizo, inda wani ma’bocin Facebook Temitope Ajayi ya ce: “Da ma ya bata kyautar motar ba tare da wani shagali ba, na menene shagalin nan haka?”

Bidiyon:

Shi kuwa Maruf Bello cewa yayi: “Yanzu wannan yana nufin a duk danginsa babu mabukata, wannan ba komai bane illa jahilci da rashin sanin ya kamata.”

Shi dai Femi Gbajabiamila yana wakiltar yankin Surulere ne a majalisar wakilan Najeriya, kuma dan jam’iyyar APC ne, wanda tun a shekarar 2003 yake majalisa, a yanzu kuma yana neman zuwa karo na biyar.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel