Magana kan Bello Turji Ya Jawo Matsala, an Zargi Yan APC da Kai Hari kan Jigon Jam'iyyar

Magana kan Bello Turji Ya Jawo Matsala, an Zargi Yan APC da Kai Hari kan Jigon Jam'iyyar

  • Jigon APC a jihar Zamfara, Dr. Sani Shinkafi ya ce an yi yunkurin kashe shi yayin walimar aure a masallacin Juma’a a Gusau
  • Shinkafi ya zargi wasu ‘ya’yan APC da hannu a yunkurin, yana danganta lamarin da tsokacin da ya yi kan Bello Turji
  • Jam’iyyar APC a Zamfara ta yi Allah wadai da harin, ta kuma tabbatar da hukunta masu hannu a wannan lamari

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Gusau, Zamfara - Wani jigo a jam’iyyar APC a jihar Zamfara, Dr. Sani Shinkafi, ya koka kan yunkurin hallaka shi da aka yi.

Dr. Shinkafi ya bayyana cewa an yi yunkurin kashe shi saboda tsokacin da ya yi kan dan ta'adda, Bello Turji.

Jigon APC ya sha da kyar bayan harin da yan jam'iyyarsa suka kai masa kan Turji
Ana zargin yan APC sun farmaki jigonsu kan sukar ayyukan Bello Turji. Hoto: Sani Abdullahi Shinkafi.
Asali: Facebook

An kai hari kan jigon APC a Zamfara

Dr. Shinkafi ya fadi haka ne yayin da yake magana da manema labarai a gidansa da ke Gusau ranar Asabar, cewar Punch.

Kara karanta wannan

Fitaccen Fasto a Najeriya ya yi aikin Hajji a Saudiyya? Adeboye ya fede gaskiya

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Dan jam'iyyar APC ya zargi ‘yan siyasa da ‘yan bindiga ne suka shirya wannan yunkuri saboda kalamansa kan matsalar tsaro.

Dr. Shinkafi ya tabbatar da cewa wasu matasa dauke da makamai sun yi yunkurin kai masa farmaki a lokacin.

“Ina cikin masallacin Rabi’a lokacin da wasu matasa suka zo dauke da makamai, suna zagina da kokarin kai mani da farmaki."
"Idan ba don jami’an tsaro da abokan siyasa na ba, da sun kashe ni."
“Ba zan bari kuskuren da ya faru a baya ya sake faruwa ba, zan ci gaba da kare adalci, ko da kuwa ya batawa wani rai."

- Dr. Sani Shinkafi

Farmaki: Jigon APC ya zargi yan jam'iyyarsa

Dr. Shinkafi ya ce wadanda suka kai masa hari ‘ya’yan APC ne, yana mai cewa wannan wani shiri ne na hana shi magana kan gazawar gwamnati wajen kama Turji, cewar Daily Post.

Shinkafi ya yi gargadin cewa ba zai daina magana kan matsalolin jihar ba, ya kuma tunatar da yadda APC ta rasa jihar Zamfara a 2019 da 2023 saboda rashin adalci.

Kara karanta wannan

Ghana: Bidiyon yadda dogarin shugaban kasa ya kife a cikin Majalisa, an kai shi asibiti

Legit Hausa ta yi magana da wani dan APC

Kwamred Saifullahi Yahaya ya ce idan har zargin da Dr. Shinkafi ya yi gaskiya ne to akwai matsala.

"Matsalar tsaro ta wuce gaban wasa, bai kamata siyasa na shiga lamarin ba saboda matsalolin da za ta haifar."

- Kwamred Saifullah Yahaya

Ya bukaci jami'an tsaro su yi bincike kan lamarin kamar yadda APC reshen jihar ta bukata.

Sanatan ya sha da kyar a Kaduna

Kun ji cewa wasu yan daba sun kai wani hari domin neman rayuwar Sanata Lawal Adamu Usman a jihar Kaduna.

Sanata Lawal Usman da ke wakiltar Kaduna ta Tsakiya a Majalisar Dattawa ya sha da kyar yayin harin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.