Sojojin Sama Sun Yi Ruwan Wuta kan 'Yan Ta'addan ISWAP, an Tura Miyagu da Dama Barzahu

Sojojin Sama Sun Yi Ruwan Wuta kan 'Yan Ta'addan ISWAP, an Tura Miyagu da Dama Barzahu

  • Ƴan ta'addan ISWAP sun gamu da gamonsu a jihar Borno da ke yankin Arewa maso Gabashin Najeriya bayan sun farmaki dakarun sojoji
  • Rundunar sojojin saman Najeriya (NAF) ƙarƙashin Operation Hadin Kai ta yi ruwan wuta kan maɓoyar ƴan ta'addan na ƙungiyar ISWAP
  • Hare-haren da sojojin saman suka kai sun yi sanadiyyar hallaka tsagerun ƴan ta'adda da dama tare da lalata babura masu yawa

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Borno - Rundunar sojojin saman Najeriya (NAF) ƙarƙashin Operation Hadin Kai, ta kai hare-hare kan ƴan ta'addan ƙungiyar ISWAP.

Rundunar sojojin saman ta yi wa ƴan ta'addan ɓarna ne bayan wani harin da suka kai wa sojoji da sanyin safiyar Asabar a Sabon Gari, ƙaramar hukumar Damboa, jihar Borno.

Sojojin sama sun sheke 'yan ta'addan ISWAP a Borno
Sojojin sama sun hallaka 'yan ta'addan ISWAP a Borno Hoto: Sodiq Adelakun
Asali: Getty Images

Masani kan harkokin tsaro a yankin tafkin Chadi da Arewacin Najeriya, Zagazola Makama ne ya bayyana hakan a shafinsa na X.

Kara karanta wannan

Fadan Fulani da makiyaya ya barke a Jigawa, an samu asarar rayuka

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda aka kai hare-hare kan ƴan ISWAP

Majiyoyin leƙen asiri sun bayyana cewa ƴan ta'addan sun ƙaddamar da harin ne da sanyin safiyar ranar Asabar, 4 ga watan Janairu, inda suka kashe sojoji aƙalla biyar kafin su koma yankin Timbuktu Triangle.

Da ake mayar da martani cikin gaggawa, an tura jiragen NAF domin kakkaɓe maharan da suka tsere.

A yayin da ake duba wurin, an hango ƴan ta'addan sun ɓoye a ƙarƙashin bishiyoyi masu duhu a Farin Ruwa, wani sansanin maɓoyar ISWAP a cikin Timbuktu Triangle.

An kai hare-haren ta sama, waɗanda suka jawo hallaka ƴan ta'adda masu yawa tare da lalata baburansu.

Sojoji sun yi ruwan wuta kan ƴan ta'addan ISWAP

A wani labarin kuma, kun ji cewa dakarun sojojin saman Najeriya sun kai hare-hare kan ƴan ta'addan ISWAP a yankin Dogon Chikun da ke jihar Borno.

A yayin harin da sojojin suka kai, an hallaka aƙalla mayaƙan ƙungiyar ta'addanci ta ISWAP guda 32 bayan an sakar musu bama-bamai ta sama.

Sojojin sun kai harin ne bayan ƴan ta'addan na ISWAP sun gwabza faɗa tsakaninsu da wani ɓangare na su, wanda ba sa ga maciji.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng