Kudirin Haraji: Malamin Musulunci Ya Ba Arewa Shawarar Gujewa Zaman Gori

Kudirin Haraji: Malamin Musulunci Ya Ba Arewa Shawarar Gujewa Zaman Gori

  • Malamin addinin musulunci, Abubakar Abdussalam Babangwale yayi lacca a game da kudirorin gyaran haraji
  • Masanin hadasin ya ba talakawa da shugabannin jihohin Arewa shawarar yadda za su kawowa yankinsu cigaba
  • Sheikh Abubakar Babangwale ya bukaci gwamnoni su kauracewa rikicin siyasa, talakawa kuma su waye da zamani

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada

Sheikh Abubakar Abdussalam Babangwale ya gabatar da lacca ta musamman da aka shirya game da kudirorin gyaran haraji.

Malamin musuluncin ya bayyana ra’ayinsa game da tsarin tare da yin kira da babbar murya ga hukumomi da mutanen Arewa.

Abubakar Abdussalam Babangwale
Abubakar Abdussalam Babangwale ya yi kira ga Arewa kan kudirin haraji Hoto: Abubakar Abdussalam Babangwale
Asali: Facebook

Lacca a kan sababbin kudirorin gyaran haraji

Cibiyar musulunci ta ITN da ke garin Zariya ta shirya laccar kwanaki, ta kuma kira malamin domin ya yi magana a mahangar addini.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sheikh Abubakar Abdussalam Babangwale ya ce tun farko Barista Adam Ishaq Adam aka so ya gabatar da laccar, amma ba a yi nasara ba.

Kara karanta wannan

Rikici ya ƙara tsanani, an gano mai zuga gwamna ya yi wa Bola Tinubu 'rashin kunya'

Wani Farfesa a ilmin akanta, Salisu Abubakar daga jami’ar Ahmadu Bello shi ne ya zama shugaban zama wajen tattaunawar da aka yi.

Mafita a kan matsalolin kudirorin haraji

A lokacin da ake zargin gwamnatin Bola Tinubu ta kawo manufofi marasa farin jini, malamin ya ba al’umma shawarwarin tsayawa da kafafu.

Na farko ya ce dole a dage da addu'a domin samun saukin matsin lambar tattalin arziki.

Sannan ya sai mutane sun tashi tsaye sujn riƙa cin ribar siyasa, a daina tunanin mulki a matsayin hanyar yanka filaye kurum a saida.

A bangaren attajirai da 'yan kasuwa kuwa, ya ce ya kamata a rika kamfanoni a Arewa.

Sannan Sheikh Baban Gwale ya kawo shawara mutanen Arewa su rika inganta kayan noma ta yadda za su ci moriyar tsarin na harajin VAT.

A nan ne ya kawo misalin yadda za a gina kasuwannin dabbobi na zamani da za su rika harkar nama, kaho, kasusuwa da sauransu.

Kara karanta wannan

"Za a ji dadi," Majalisa ta fadi yadda amincewa da kudirin haraji zai canja Najeriya

Idan aka dauki salon nan, ko da an canza tsarin kason harajin VAT da ake ta surutu a kai, malamin ya ce jihohin Arewa za su samu kudi.

Baban Gwale ya ce sai shugabanni sun hakura da takarar gina gadoji, su kawowa al’umma cigaba domin Ubangiji zai tambaye su a kiyama.

Kira ga talakawa da matasan Arewa

Ga sauran al’umma, ya ce akwai bukatar a kafa kungiyoyin fararen hula da za su tsaya domin tasa gwamnatocin Najeriya su yi abin da ya dace.

Sannan ya ba matasa shawara su yi karatun zamani su samu shaida sannan su shiga kungiyoyin kwarewa ta yadda za a amfana da su.

Sheikh Baban Gwale ya soki kudirin haraji

A baya kun ji labari cewa Sheikh Abubakar Abdussalam Babangwale ya na ganin akwai rashin adalci wajen rabon harajin VAT a Najeriya.

Malam Baban Gwale ya yi kira ga shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu da ‘yan majalisar tarayya su sake nazarin kudirin domin a zauna kalau.

A wata lacca da ya yi, malamin ya fallasa yadda ma’aikata za su yi fama da biyan haraji duk da ikirarin gwamnati cewa an dauke masu nauyi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng