'Abin da Ya sa Yar'adua Soke Siyar da Matatar Mai ga Dangote da Obasanjo Ya Roka'

'Abin da Ya sa Yar'adua Soke Siyar da Matatar Mai ga Dangote da Obasanjo Ya Roka'

  • Lauya a Najeriya, Femi Falana ya fadi dalilin da marigayi tsohon shugaban kasa, Umaru Yar’Adua ya soke sayar da matatar mai ta Port Harcourt
  • Fitaccen lauyan ya ce marigayin ya dauki matakin ne saboda rashin bin ka’ida da kuma yajin aiki
  • Wannan na zuwa bayan tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo ya Yar'Adua ya ki amincewa da alfarmar da ya nema wa Aliko Dangote

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Babban Lauya a Najeriya, Femi Falana ya yi magana kan kin siyar da matatar mai ta Port Harcourt da ke Rivers

Lauyan ya ce marigayi tsohon shugaban kasa, Umaru Yar’Adua ya soke sayar da matatar ga wata kungiyar kasuwanci da Aliko Dangote saboda rashin bin doka.

Lauya ya fadi yadda Yar'Adua ya soke siyar da matatar mai ga yan kasuwa
Lauya Femi Falana ya soki Obasanjo kan saba ka'ida inda ya yabawa marigayi Yar'Adua. Hoto: Olusegun Obasanjo, Femi Falana, Pius Utomi Ekpei.
Asali: Getty Images

Yadda Yar'Adua ya ki saba ka'ida kan matata

Kara karanta wannan

Matasa sun lakadawa basarake duka kan nada limamin Juma'a, an ceto rayuwarsa

Punch ta ce lauyan ta tabbatar da cewa matakin na Yar’Adua ya nuna tsayuwa kan kare muradun kasa da bin ka’idojin doka a sayar da kadarorin gwamnati.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Falana ya ce, bisa ga dokar siyar da matatar ga yan kasuwa, mataimakin shugaban kasa ne ke jagorantar kwamitin da ke kula da sayar da kadarorin gwamnati.

Sai dai ya zargi Olusegun Obasanjo da kaucewa wannan doka, inda ya mayar da tsarin hannunsa, ya yi watsi da Atiku Abubakar.

'Obasanjo ya saba ka'ida a ciniki' - Falana

Lauyan ya ce Obasanjo ya sayar da 51% na hannun jari a matatar mai ta Port Harcourt da Kaduna ga kungiyar Bluestar Oil.

Wannan yarjejeniyar ta haifar da ce-ce-ku-ce daga kungiyoyin kwadago, wadanda suka yi zargin cewa an yi wa kasa kutse.

A cewar sanarwar, kungiyoyin kwadago sun fara yajin aiki na kwanaki hudu don nuna rashin amincewa da sayar da kadarorin, cewar TheCable.

Kara karanta wannan

Yadda tsohon shugaban Amurka ya ceci rayuwar Obasanjo har ya rayu zuwa yanzu

Sun kuma yi zargin cewa darajar hannun jarin matatar mai ya ninka farashin da aka sayar da ita wanda ya sa gwamnatin Yar’Adua ta soke yarjejeniyar.

Yadda Obasanjo ya roki marigayi Yar'Adua alfarma

Kun ji cewa tsohon Shugaban Ƙasa, Olusegun Obasanjo, ya bayyana yadda marigayi Umar Musa Yar’adua ya ki amincewa da tayin Aliko Dangote na gudanar da matatun mai.

Olusegun Obasanjo ya ce Dangote ya shirya tawaga kuma suka biya Dala miliyan 750 domin gudanar da matatun man Najeriya karkashin haɗin gwiwa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.