Babban Albishiri Ga ’Yan Najeriya: Akwai Yiwuwar Man Fetur Ya Koma N500 a Lita Nan Kusa
- Dillalan man fetur da sauran kwararru a masana'antar man fetur sun yi hasashen cewa za a rage farashin man fetur a shekarar 2025 zuwa N500 a lita
- Dawowar aikin matatar man fetur ta Port Harcourt da Warri zai taimaka wajen rage farashin man a Najeriya
- Sun jaddada cewa samar da kayayyakin man fetur cikin tsayayyen lokaci zai karfafa gasar da ke tsakanin masu ruwa da tsaki a harkar, wanda zai haifar da karin rage farashi
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Najeriya - Dillalan man fetur da sauran masu ruwa da tsaki a masana'antar man fetur a Najeriya sun yi hasashen cewa za a samu ragin farashin man fetur sosai a shekarar 2025.
Sun bayyana cewa man fetur, wanda a halin yanzu yake tsakanin N900 da N950 a kowace lita a yawancin gidajen mai, zai iya sauka har zuwa N500 a kowace lita a wannan shekarar.
Maganar da kwararru ke yi kan farashin mai
A cewar kwararru a masana'antar, wannan ragin da ake sa ran zai faru yana da nasaba da karfafa bangaren masana'antar man fetur, wanda gwamnatin tarayya ta aiwatar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wasu daga cikin dalilan da za su taimaka wajen rage farashin sun hada da kwararar kudaden waje mai dorewa, karuwar gasa a tsayar da farashin, tsarin naira-da-man fetur, da kuma dawowa bakin aiki na matatun man fetur na Port Harcourt, Warri, da Dangote.
Masu ruwa da tsaki sun kara da cewa idan wadannan matatun man fetur sun samar da kayayyakin man fetur a cikin kasuwar cikin gida kuma suka karbi kudinsu da naira, zai taimaka wajen rage farashin man fetur.
Dalilan da mai zai iya sauka nan kusa
Sakataren yada labarai na kasa na Kungiyar Masu Siyar da Man Fetur Najeriya (IPMAN), Ukadike Chinedu, ya bayyana dawowa bakin aiki da matatun mai na Port Harcourt da Warri a matsayin wani canji mai muhimmanci ga bangaren mai.
A cikin wata hira da Saturday Sun, ya jaddada cewa wadannan matatun man fetur za su karfafa gasa mai kyau a tsayuwar farashi, wani yanayi da ake ganin yana bayyana a yanzu.
Ya nuna cewa Kamfanin Man Fetur na Kasa (NNPC) da Dangote sun rage farashin man fetur a makon baya, yana mai jaddada amfanin samun hanyoyin samar da man da yawa maimakon mamayar wani tsagi daya.
Ci gaban da za a samu nan kusa a fannin man fetur
Ukadike ya ce yana da kwarin gwiwar cewa wannan ci gaban zai iya sa farashin man fetur ya sauka kasa da N500 a kowace lita a shekarar 2025 yayin da karin masu shigar da kaya za su inganta ikon sarrafa man fetur.
Ya kuma bayyana manufofin gwamnatin tarayya na alakar naira-da-man fetur a matsayin muhimmin abu wajen tsara farashin man fetur, yana mai hasashen cewa wannan zai taimaka wajen dakatar da hauhawar farashin kayayyaki da kuma rage matsi da tsananin bukatar kudaden waje.
Shugaban kungiyar mai ta PETROAN, Billy Gillis-Harry, ya amince da ra'ayoyin Ukadike.
Ya tabbatar da cewa fara aikin matatun man fetur na Port Harcourt da Warri zai haifar da karin saukin farashin mai ga 'yan Najeriya.
Yadda gasa a fannin samar da mai zai taimaki jama'a
Gillis-Harry ya jaddada cewa cimma farashin man fetur mai sauki ga ‘yan kasa zai zama wata dama mai kyau a shekarar 2025.
Gillis-Harry ya ce:
"Kamar yadda kuka gani, NNPC ta rage farashin sari daga N1,045 kowace lita zuwa N899 kowace lita ga dillalai, wanda yake nufin N925 kowace lita a gidajen mai ga masu amfanin yau da kullum.
“Da wannan, nake cewa, abu ne mai kyau sosai. Wannan ba karamin ragi ba ne, ragi ne mai yawa daga N1,045 zuwa N899."
Makomar farashin man fetur a 2025
Ya jaddada cewa samar da man fetur cikin tsayayyen lokaci zai karfafa gasa, wanda zai sa farashin ya ragu a cikin shekarar ta 2025.
A nasa bangaren, sakataren yada labarai na Kungiyar Masu Sarrafa Man Fetur na Najeriya (CORAN), Iche Idoko, ya bayyana cewa 'yan Najeriya za su fara jin dadin amfanin farashin da aka sassauta.
Idoko ya ce:
"Ragin farashin daya daga cikin alamu ne na warware matsin kasuwan da muka bayyana. Yayin da masana'antar ta tsaya daram kan tsarin warware kasuwa matsin farashi gaba daya, za mu ga gasa tsakanin masu ruwa da tsaki, wanda daga karshe zai amfanar da jama’a."
Ba yanzu aka fara hasashen komar farashin man fetur N500 ko N600 ba, an yi hakan a baya amma ba a cimma ba.
Asali: Legit.ng