Shettima da Manyan Yan Siyasa Sun Dura a Kano, Mataimakin Gwamna Abba Ya Tarbe Su

Shettima da Manyan Yan Siyasa Sun Dura a Kano, Mataimakin Gwamna Abba Ya Tarbe Su

  • Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima ya halarci daurin auren 'ya'yan shugaban APC na Kano, Alhaji Abdullahi Abbas
  • Shettima ya samu tarba daga mataimakin gwamnan Kano, Aminu Abdussalam Gwarzo, da mataimakin shugaban majalisar dattawa, Barau Jibrin
  • An gudanar da daurin auren a Masallacin Al-Furqan, inda ya yi addu’o’in fatan alheri da nasara ga ma’auratan

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Kano - Mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima ya halarci bikin daurin auren 'ya'yan shugaban jam'iyyar APC reshen jihar Kano, Alhaji Abdullahi Abbas.

An gudanar da bikin daurin auren ne a ranar Asabar 4 ga watan Janairun 2024 a masallacin Al-Furqan.

Shettima ya halarci daurin auren 'ya'yan shugaban APC a Kano
An daura auren 'ya'yan shugaban APC a Kano, Shettima ya samu halartar bikin. Hoto: @stanleynkwocha.
Asali: Twitter

Shettima ya shiga Kano daurin aure

Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da mataimakin Shettima a bangaren sadarwa, Stanley Nkwocha ya wallafa a shafin X.

Kara karanta wannan

Peter Obi ya ziyarci IBB, ya bayyana abubuwan da suka tattauna a kan Najeriya

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shettima ya isa garin Kano ta filin jirgin sama na Mallam Aminu Kano, inda ya samu kyakkyawar tarba daga manyan mutane.

Daga cikin wadanda suka tarbe shi har da mataimakin gwamnan Kano, Aminu Abdussalam Gwarzo.

Sai kuma mataimakin shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau Jibrin da tsohon mataimakin gwamnan Kano, Nasir Yusuf Gawuna.

An daura auren Abbas Abdullahi Abbas da amaryarsa, Khadija Attahire Buhari, da kuma Muhammad Abdullahi Abbas da amaryarsa Zulaihat Nasir (Mimi).

Malamin da ya jagoranci daurin auren a Kano

Babban limamin masallacin Al-Furqan, Sheikh Dr. Bashir Aliyu Umar, ne ya jagoranci daurin auren.

A lokacin bikin, Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima ya wakilci Muhammad yayin da Sanata Barau Jibrin, ya wakilci Abbas.

An kammala bikin da addu’o’in fatan alheri ga ma’auratan da addu'ar Allah ya albarkaci zaman aurensu da zaman lafiya da albarka.

Kalli hotunan daurin auren a kasa:

Kashim Shettima

Kara karanta wannan

Mutane da dama sun samu raunuka da aka tsige shugabannin kananan hukumomi 2

Kashim Shettima

Kashim Shettima

Kashim Shettima

Tinubu ya ba da auren yar Barau

A baya, kun ji cewa manyan 'yan siyasa da dattawa sun halarci bikin daurin auren yar Sanata Barau Jibrin a birnin Abuja.

An daura auren ne tsakanin iyalan Barau da na tsohon Sarkin Bichi, Nasir Ado Bayero a masallacin Abuja.

Tinubu shi ne ya kasance waliyyi ga ya'yan Sanata Barau duka biyu ta hannun shugaban Majalisar Dokoki, Hon. Tajudden Abbas.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.