Rai Bakon Duniya: Kadan Daga Abinda Baku Sani ba Game da Mace Mafi Tsufa a Duniya da ta Kwanta Dama
- Tomiko Itooka, wata mata daga kasar Japan da aka taba alantawa a matsayin mafi tsufa a duniya a Guinness World Records, ta rasu tana da shekara 116
- Matar da aka Haifa a watan Mayun 1908, ta rayu tun daga yakin duniya biyu har zuwa annobar COVID-19, kuma ta shaida ganin ci gaban fasaha mai yawa
- Bayan rasuwarta, ana ganin Inah Canabarro Lucas daga Brazil mai shekaru 116, ita ce mafi tsufa a duniya a yanzu, ko da yake Guinness World Records bata tabbatar ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Kasar Japan — Tomiko Itooka, wata mata daga kasar Japan da aka ayyana a matsayin mafi tsufa a duniya a Guinness World Records (GWR), ta rasu a shekara 116.
Hukumomi sun bayyana cewa Itooka ta rasu ne a gidan kula da marasa lafiya da tsofaffi a garin Ashiya, cikin lardin Hyogo ta kasar Japan.
Legit.ng ta ruwaito cewa GWR ta gamsu tare da alanta Itooka a matsayin mace mafi tsufa a duniya bayan rasuwar Maria Branyas Morera daga kasar Spain a watan Agustan 2024, wadda ta rasu tana da shekaru 117.
Tomiko Itooka ta ba mu karfin gwiwa, inji Takashima
A bangare guda, magajin garin Ashiya, Ryosuke Takashima, ya yi martani game da rasuwar wannan baiwar Allah da ta ga duniya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Magajin garin mai shekaru 27 ya shaidawa BBC cewa:
“Ms. Itooka ta ba mu karfin gwiwa da fata a more rayuwarta mai tsawo. Muna gode mata bisa wannan.”
GWR ta kuma tabbatar da rasuwar Itooka.
A wani sakon da ta wallafa a kafar X, GWR ta bayyana cewa:
“Labari mara dadin ji a yau cewa mace mafi tsufa a duniya, Tomiko Itooka, ta rasu a shekara 116. Muna yiwa iyalinta ta’aziya.”
A cewar jami’an, an gudanar da hidimar jana’izarta tare da dangi da abokai.
Waye Tomiko Itooka?
An haifi Misao Itooka a watan Mayu 1908, ta rayu inda ta shaida yakin duniya biyu da kuma annobar COVID-19, kuma ta ci karo da kusan dukkan gaban fasaha da aka samu a tsawon lokacin, wanda ya hada da kaddamar da motar Ford Model T a Amurka a shekarar da aka haife ta.
GWR ta tabbatar da Itooka a matsayin mafi tsufa a duniya a watan Satumba 2024 kuma an ba ta takardar shaida ta musamman a Ranar Karrama Tsofaffi da ake gudanarwa a kasar Japan.
A cewar jami’an cikin gida, Itooka ta yi rayuwa mai kyau a matakin matasantaka, tana buga kwallon volleyball da kuma hawan Dutsen Ontontake, wanda yake da tsayin mita 3,067 (kafa 10,062), ta hau sau biyu.
A baya-bayan nan, abincinta mafi soyuwa ya hada da ayaba da Calpis, wani shahararren abin sha na ‘yan kasar Japan.
Itooka ta yi aure tana shekara 20, ta haifi yara hudu, wanda biyu suka rayu; mace daya da namiji daya. Hakanan tana da jikoki guda biyar.
Waye mafi tsufa a duniya bayan rasuwar Tomiko Itooka?
BBC ta ruwaito cewa Inah Canabarro Lucas, daga kasar Brazil, wadda aka haifa kwanaki 16 bayan haihuwar Itooka kuma tana da shekaru 116 yanzu, ana ganin ta yanzu ita ce mace mafi tsufa a duniya. Sai dai, GWR bata tabbatar da wannan batu ba tukuna.
GWR na yawan adana bayanai da kiyaye su kan mutanen da suka fi tsufa a duniya, kuma akan alanta na gaba da zarar wanda ke rike da kambin ya rasu.
Asali: Legit.ng