Gwamnan PDP Ya ba Kanin Nuhu Ribadu Muƙamin Sarki, Ya ba Sarakunan Shawara

Gwamnan PDP Ya ba Kanin Nuhu Ribadu Muƙamin Sarki, Ya ba Sarakunan Shawara

  • Gwamna Ahmadu Umaru Fintiri ya nada Sani Ahmadu Ribadu, dan uwa ga Malam Nuhu Ribadu, matsayin sabon Sarkin Fufore
  • Sababbin masarautun guda bakwai sun hada da masarautu masu daraja ta biyu da wasu sarautu masu daraja ta uku da aka kirkira a Adamawa
  • Gwamnan ya bukaci sababbin sarakunan su kasance masu gaskiya, adalci, da rikon amana wajen gudanar da ayyukansu

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Yola, Adamawa - Gwamnan jihar Adamawa, Ahmadu Umaru Fintiri, ya nada Sani Ahmadu Ribadu a matsayin sarkin Fufore.

Sani Ribadu dan uwa ne ga mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro, Nuhu Ribadu.

An nada kanin Ribadu sarautar gargajiya
Gwamna Ahmadu Fintiri ya nada kanin Nuhu Ribadu sarautar gargajiya a Adamawa. Hoto: @NuhuRibadu, @GovernorAUF.
Asali: Twitter

Kanin Nuhu Ribadu ya zama sarki a Adamawa

Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da gwamnan ya wallafa a shafin X a jiya Juma'a 3 ga watan Janairun 2025.

Kara karanta wannan

Tsohon ‘dan APC ya bada labarin yadda aka rabawa Buhari hankali da takarar Tinubu

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Nadin na daya daga cikin sababbin sarautu guda bakwai da aka kirkira a jihar, wanda ya hada da sababbin masarautu guda biyu da wasu guda biyar.

Sababbin sarakunan sun hada da Sani Ahmadu Ribadu (Sarkin Fufore) da Alheri Nyako (Tol na Huba) da Bulus Luka Gadiga (Mbege na Michika) da Ali Danburam (Ptil na Madagali).

Sai kuma John Dio (Gubo Yungur) da Aggrey Ali (Kumu na Gombi) da Ahmadu Saibaru (Sarkin Maiha).

Wannan ya biyo bayan kokarin da gwamnatin jihar ta yi na kara inganta tsarin masarautu domin amfanin al'umma.

Mai magana da yawun gwamna, Humwashi Wonosikou, ya bayyana cewa an zabi sabbin sarakunan ne bisa cancanta da amincewar jama'a.

Gwamna Fintiri ya ba sababbin sarakuna shawara

Gwamnan ya bukaci sabbin sarakunan su kasance masu gaskiya, adalci, da rikon amana.

"Gwamna Fintiri ya taya sabbin sarakunan murna, yana mai tabbatar da cewa nadin nasu ya samu ne bisa cancanta da goyon bayan jama'a.

Kara karanta wannan

Rikici ya ƙara tsanani, an gano mai zuga gwamna ya yi wa Bola Tinubu 'rashin kunya'

"Wannan nadin sababbin sarakunan ya fara aiki nan take."

Cewar sanarwar

Gwamna Fintiri ya kirkiri sababbin masarautu

A wani labarin, Gwamna Ahmadu Fintiri na jihar Adamawa ya kirkiro sababbin masarautu masu daraja ta biyu da masu daraja ta uku guda bakwai.

Ahmadu Fintiri ya ce ya yi haka ne ba don kara faɗaɗa ayyukan sarakuna waɗanda ke ba da gudummuwa ta fannoni daban-daban.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.