Fitaccen Fasto a Najeriya Ya Yi Aikin Hajji a Saudiyya? Adeboye Ya Fede Gaskiya

Fitaccen Fasto a Najeriya Ya Yi Aikin Hajji a Saudiyya? Adeboye Ya Fede Gaskiya

  • Babban Limamin Cocin RCCG, Pastor Enoch Adeboye, ya magantu kan hoton AI da ya nuna shi a matsayin Alhaji
  • Hoton AI din da aka yada ya jawo martani a dandalin sada zumunta, inda mutane da dama suka yi martani kansa
  • Faston ya yi kira ga masu shekaru sama da 70 su guji azumi mai tsanani, inda ya yi tsokaci kan shirin shekara ta 2025

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Lagos - Babban Limamin Cocin Redeemed Christian Church of God (RCCG), Pastor Enoch Adeboye ya yi martani kan hoton da ake yaɗawa yana aikin hajji.

Faston ya yi fatali da hoton AI da ke yawo a kafafen sada zumunta, wanda ya nuna shi a matsayin Alhaji.

Fasto Adeboye ya yi magana kan hotonsa yana aikin hajji
Fasto Enoch Adeboye ya musanta hotonsa da ake yadawa yana aikin hajji. Hoto: Pastor Enoch Adeboye.
Asali: Twitter

Fasto ya magantu kan hotonsa a hajji

A cewar Punch, Adeboye ya yi wannan jawabi a taron 'Holy Ghost Night' na farko na sabuwar shekara, wanda aka gudanar da asubahin ranar Asabar, 4 ga Janairu.

Kara karanta wannan

Ghana: Bidiyon yadda dogarin shugaban kasa ya kife a cikin Majalisa, an kai shi asibiti

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A watan Disambar 2024, an yada wasu hotuna da ke nuna Pastor Adeboye a cikin kayan Musulunci a Makkah da ke Saudiyya.

Hotunan da aka kirkira da fasahar AI sun jawo ce-ce-ku-ce a yanar gizo, inda wani mai amfani da X, @Sarkideyforyou ya wallafa hoton Adeboye a gaban Ka’aba a Makkah s.

Matashin ya rubuta cewa:

“Pastor Adeboye, Allah ya shiryar da kai zuwa hanya madaidaiciya.”

Wannan wallafa ta samu karbuwa sosai, inda mutane miliyan 3.8 suka kalla, tare da jawo maganganu a yanar gizo.

Cikin murmushi, Fasto Adeboye ya yi magana kan hoton AI da aka yi ta yaɗawa a kafofin sadarwa:

“Na tabbata da dama daga cikinku sun ga hoton da ke nuna ni a matsayin Alhaji.”

- Fasto Enoch Adeboye

Fasto ya yi hasashen shekarar 2025

Faston ya tabbatar wa masu taron cewa shekarar 2025 za ta zama mai cike da canje-canje masu muhimmanci a rayuwa, tare da tabbatar da maganar Allah.

Kara karanta wannan

'Ku dage da addu'a;" Malamin addini ya hango abin da zai faru da Najeriya a 2025

Ya shawarci tsofaffi sama da shekaru 70 su guji azumi mai tsanani, inda ya ce wadanda ke tsakanin shekaru 70 zuwa 80 su karya azumi da karfe 3 na rana.

Fasto ya fadi taimakon Najeriya da Allah ya yi

Mun ba ku labarin cewa jagoaran cocin RCCG, Fasto Enoch Adeboye ya bayyana cewa babu abin da Najeriya ta fi bukata a yanzu kamar addu'a.

Da yake jawabi a wani taro a Abuja, Malamin cocin ya ce ba don taimakon Allah ba da yanzun canjin Dala ya kai N10,000.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.