'Yan Bindiga: Limamin da Ake Fargabar Ya Bace, Ya Bayyana Kwatsam bayan Kwanaki 25

'Yan Bindiga: Limamin da Ake Fargabar Ya Bace, Ya Bayyana Kwatsam bayan Kwanaki 25

  • Godwin Okpala ya fito daga hannun ‘yan bindiga da ake zargin sun yi garkuwa da shi a karshen bara
  • An daina jin duriyar Faston da direbansa ne a lokacin da suka yi wata tafiya zuwa Umuchu a garin Aguata
  • Babu tabbacin ko Fasto Godwin Okpala ya biya wasu kudi fansa kafin ya kubuta daga hannun ‘yan bindigan

Anambra - Wani babban fasto a cocin angilikan da aka shiga fargabar ya bace a watan da ya gabata, ya sake bayyana a halin yanzu.

Godwin Okpala wanda tsohon archbishop ne a jihar Neja kuma Bishof a yankin Nnewi jihar Anambra ya fada hannun 'yan bindiga.

Fasto
'Yan bindiga sun dauke malamin addinin kirista a Anambra Hoto: Anglican Diocese of Awka
Asali: Facebook

'Yan bindiga sun sako Fasto a Anambra

Bayanan da aka samu daga shafin cocin Living Church a yanar gizo ya nuna cewa limamin ya kubuta daga hannun wadanda suka tsare sa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A ranar ga watan Disamba, Godwin Okpala wanda Farfesa ne a jami’a ya yi tafiya zuwa garin Umuchu, tun lokacin ba a sake ganinsa ba.

Kara karanta wannan

Daga zuwa sasanta rikicin miji da mata, an kashe wani malamin addini a Najeriya

Hankalin almajiran Godwin Okpala ya tashi

Sa’ilin da abin ya faru, Farfesa Godwin Okpala ya na tare da direban motarsa. Tun lokacin hankalin almajirai da ‘yanuwa da abokai ya tashi.

Kwanaki kimanin 25 da bacewar malamin addinin kiristan, sai ga shi cewa ya sake bulla.

Premium Times ta ce Mista Okpala ya sanarwa duniya cewa ya dawo da wani rubutu da ya yi a safiyar ranar Alhamis a shafinsa na Facebook.

Malamin yake cewa ‘A godewa Ubangiji’, wannan ya kwantar da hankalin mabiyansa.

Ba a dade ba kuma sai ga cikakken bayani daga shafin mabiya darikar Angilikan na reshen garin Awka a Anambra, aka tabbatar da labarin.

Addu'a ta yi wa 'yan bindiga tasiri?

Anglican Diocese of Awka sun ce fitowar malamin da direbansa ya nuna irin karfin addu’a.

A jawabin da aka fitar, cocin ya ce lamarin ya kara nuna akwai bukatar a yi garambawul wajen yadda ‘yan sanda ke aiki a Najeriya.

Kara karanta wannan

An shiga tashin hankali: Malamin addini ya sa bindiga ya harbe wani yaro har lahira

Cocin ya taya al’umma da sauran dinbin masoya dawowar limamin da kuma direbansa.

Ana ganin cewa ba wannan ne karon farko da aka yi garkuwa da mutane a Kudu maso gabas ba don haka ya kamata a tashi tsaye sosai.

Shugaban Nijar ya tara bokaye a fada

Janar Abdourahamane Tchiani ya buge da tara bokaye da nufin ganin bayan makiyan kasar Nijar kamar yadda rahoto ya gabata a baya.

Kungiyar bokaye ta yi zama a Niamey kuma sun yi wa Abdourahamane Tchiani alkawarin za su yi amfani da aljanu domin biya masa bukata.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng