Mutanen Abuja Za Su Ji Yadda Talakawa Ke ciki, Za a Samu Matsalar Wuta na Kwanaki

Mutanen Abuja Za Su Ji Yadda Talakawa Ke ciki, Za a Samu Matsalar Wuta na Kwanaki

  • KKamfanin AEDC ya sanar da mutanen da ke zama a Abuja da Nasarawa cewa za a yi wasu gyare-gyaren wutar lantarki
  • A sakamakon haka za a shafe fiye da makonni biyu ana samun matsalar wuta a wasu unguwannin da ke Abuja
  • Lamarin zai shafi rukunin gidaje da-dama da unguwannin Apo, Bwari, Kubwa, Nyanya, Mararaba har zuwa Keffi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada

Abuja - Kamfanin AEDC da ke raba wutar lantarki a Abuja da kewayen birnin tarayya ya sanar da cewa za a yi gyare-gyare.

Wannan gyara da za a yi zai jawo a samu matsalar wutar lantarki a Abuja daga ranar Litinin zuwa 21 ga watan Junairun 2025.

Abuja
Za a iya samun matsalar wutar lantarki a Abuja Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

Za a yi gyaran wutar lantarki a Abuja

The Cable ta ce kamfanin AEDC ya fitar da jawabi cewa za a samu matsalar daukewar wuta a wuraren da ke karkashin FCDA.

Kara karanta wannan

Korar Kwankwaso daga NNPP da manyan abubawa 5 da suka faru a siyar Najeriya a 2024

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Daga ranar Litinin mai zuwa babu mamaki a ga wuta ta na daukewa a wasu unguwanni.

Abin da zai jawo hakan shi ne dauke nauyi daga wasu tashoshi na 33KV DC Airport Feeder da 132KV Kukwaba-Apo a birnin Abuja.

Ko a karshen shekarar da ta gabata, an samu makamancin wannan matsala a sakamakon gyaran da kamfanin TCN ya yi a yankin.

A ranar Juma’a, Premium Times ta kawo jerin sunayen unguwannin birnin tarayya na Abuja da wannan gyare-gyaren zai shafa.

Su wanene unguwannin Abuja da gyaran zai shafa?

Gyaran da za a yi zai taba mutanen Kewayen Lugbe, unguwannin da ke kan titin filin jirgin sama, Kapwa, NNPC sai Games Village.

Za a iya samun matsalar lantarkin a babban filin wasa na kasa na Mashood Abiola.

Kamfanin AEDC ya fadawa mutanen Asibitin ido, filin wasa, cocin Christ Embassy da makarantar American Int'l School su shirya.

Akwai Spring Court da rukunun gidajen ofishin jakadancin kasar Amurka, hedikwatar EFCC, Coca Cola, Railway da kuma asibitin FMC.

Kara karanta wannan

PDP, Obi sun ba Tinubu lakanin samo waraka daga matsalolin Najeriya

Sai kewayen Gbazango Kubwa da Bwari da yankunan Jahi, Jabi, Karu, Nyanya, Mararaba da irinsu Apo da Gudu sai Keffi a jihar Nasarawa.

An karyata zancen karin kudin wuta

A shekarar bara ne aka samu labari cewa an bayyana cewa babu wani shiri na karin kudin kamar yadda ake jita-jita a garuruwa da-dama.

Rade-radin da ake ta yi na karin kudin wuta ya kare bayan an ji AEDC ta karyata shirin canza farashi lokacin da mutane ke neman rage farashi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng