Bidiyon Abin da Mutane Suka Yi Wa Bola Tinubu bayan Gama Sallah a Masallacin Juma'a

Bidiyon Abin da Mutane Suka Yi Wa Bola Tinubu bayan Gama Sallah a Masallacin Juma'a

  • Shugaban kasa, Bola Tinubu ya gaisa da ɗaruruwan Musulmi bayan Sallar Juma'a a babban masallacin jihar Legas
  • A wani faifan bidiyo da fadar shugaban kasa ta fitar, an ga yadda mutane suka yi dafifi domin gaida shugaban ƙasa a masallaci
  • Bola Tinubu, wanda ke hutu a mahaifarsa jihar Legas, ya ɗagawa mutane hannu alamun ya amsa gabanin ya shiga mota

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Legas -Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya yi sallar Juma'a a babban masallacin jihar Legas da ke Lagos Island jiya 3 ga watan Janairu, 2025.

Har yanzu dai shugaban kasar na gidansa da ke Legas tun da ya tafi hutun kirismeti da sabuwar shekara a makon da ya gabata.

Bola Ahmed Tinubu.
Shugaba Tinubu ya amsa gaisuwar ɗaruruwan mutane bayan sallar Juma'a a jihar Legas Hoto: @DOlusegun
Asali: Twitter

Ɗaruruwan mutane ne suka yi dafifi a ciki da wajen masallacin, inda suka rika ɗagawa Shugaba Tinubu alamar alamar gaisuwa bayan kammala sallar Juma'a.

Kara karanta wannan

Rikici ya ƙara tsanani, an gano mai zuga gwamna ya yi wa Bola Tinubu 'rashin kunya'

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mai taimaka wa shugaban ƙasa kan harkokin soshiyal midiya, Dada Olusegun ya wallafa bidiyon soyayyar da aka nuna wa Tinubu a masallaci a shafinsa na X.

Bola Tinubu ya amsa gaisuwar jama'a

A faifan bidiyon, shugaba Tinubu ya amsa gaisuwar jama'a tare da ɗaga masu hannu kafin ya shiga mota ya koma gida.

Hadimin shugaban ƙasar ya ce:

"Mai girma shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ya amsa gaisuwar masu ibada bayan kammala Sallar Juma'a a babban masallacin Lagos dake Legas Island."

Martanin ƴan Najeriya kan bidiyon

Wani mai suna Olusegun ya ce:

"Ban cika son ganin mutane suna kusantar Shugaba Tinubu ba, na san jami'an tsaro ns iya bakin kokarinsu, Allah ya kara ksre shi. ya ba shi nassra, Allah ɗaga Najeriya."

Ola Michael ya ce:

"Duk waɗannan dandazon jama'ar da aka biya don su taru a wurin ba su da wani amfani a wurin masu hankali."

TJ Cool ya ce:

Kara karanta wannan

Ghana: Bidiyon yadda dogarin shugaban kasa ya kife a cikin Majalisa, an kai shi asibiti

"Ƴan Najeriya na kwarin guiwa a kansa kuma aminta da shi, Allah ya albarkacu Jagaban."

Protestass kuma ya ce:

"Sun ci gaba da yaudarar wannan mutumin, Allah kaɗai ya san daga ina aka tattaro waɗannan mutanen."

Bola Tinubu zai kai ziyara Enugu

A wani labarin, kun ji cewa Shugaba Tinubu zai kai ziyarar yini guda zuwa jihar Legas ranar Asabar, 4 ga wstan Janairu, 2025.

Gwamnatin jihar Enugu ta bayyana cews yayin wannan ziyara, shugaban kasar xai kaddamar da wasu muhimman ayyuka na Gwamna Peter Mbah ya gama.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262