'Ka da Ku Yarda': Shugaban Izalah Ya Ja Kunnen Malaman Nijar da Najeriya kan Rigima

'Ka da Ku Yarda': Shugaban Izalah Ya Ja Kunnen Malaman Nijar da Najeriya kan Rigima

  • Yayin da alaka ke kara tsami tsakanin Najeriya da Nijar, shugaban kungiyar Izalah ya ba malaman Sunnah shawara
  • Sheikh Abdullahi Bala Lau ya nuna damuwa kan yadda malamai da kansu ke jifan yan uwansu game da rigimar da ke faruwa
  • Malamin ya bukaci malaman da ka da su manta da alakar Musulunci da ke tsakaninsu saboda kawai siyasa

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Shugaban kungiyar Izalah a Najeriya, Sheikh Abdullahi Bala Lau ya yi tsokaci kan rigimar da ke faruwa tsakanin Najeriya da Nijar.

Sheikh Bala Lau ya ce abin takaici ne yadda ake neman mantawa da alaka ta Musulunci saboda siyasa.

Shugaban Izalah ya shawarci malaman Nijar da Najeriya kan rigimar da ke faruwa
Sheikh Abdullahi Bala Lau ya shawarci malaman Nijar da Najeriya kan kame bakunansu. Hoto: Abdullahi Bala Lau.
Asali: Facebook

Bala Lau ya magantu kan alakar Najeriya da Nijar

Malamin ya bayyana haka ne a cikin wani faifan bidiyo da shafin Karatuttukan Malaman Sunnah ya wallafa a shafin Facebook.

Kara karanta wannan

"Wahalarku ba za ta tafi a banza ba," Tinubu ya aika sakon 2025 ga 'yan Najeriya

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cikin bidiyon, malamin ya bukaci malaman kasashen biyu su kame bakunansu daga jifan yan uwansu saboda magana ta siyasa.

Ya ce shugabannin siyasa a dukan kasashen suna iya barin ofs amma dangantaka ta Musulunci ba ta da iyaka.

Kira zuwa ga mutanen Nijar da Najeriya

"Ina kira ga malamanmu na Najeriya mu yi kyakkyawan zato ga makotanmu na Nijar."
"Ina kira ga malamanmu na Alhlus Sunnah kan wata kofa da ke son budewa game da wasu kalmomi da suka fito daga shugaban Nijar da Najeriya saboda siyasa."
"Ka da wannan abu da ke faruwa tsakanin shugabannin gwamnati wadanda suna iya wucewa amma zumunci da dangantaka na Musulunci ba ta wucewa."

- Sheikh Bala Lau

Sheikh Bala Lau ya shawarci malamai

Sheikh Bala Lau ya ce akwai bukatar malaman Sunnah wadanda su ne suka yi kokarin kwantar da rigima lokacin da aka yi juyin mulki su kame bakunansu daga jifan juna kan rigimar.

Kara karanta wannan

An nemi karrama sarakunan Arewa da suka yaki turawan mulkin mallaka

Malamin ya ce malaman na kokarin kare kasashensu yayin da aka ajiye babin yan uwantaka na Musulunci saboda siyasa.

Zargin Tchiani: Sheikh Albaniy ya bukaci bincike

A baya, kun ji cewa, Sheikh Adam Muhammad Albaniy Gombe ya magantu kan zarge-zargen da shugaba, Abdourahamane Tchiani ya yi kan Najeriya.

Sheikh Albaniy ya ce Tchini zai iya yin kuskure duba da cewa shi ba mala'ika ba ne ko wani Aannabi da komai ya fada ba zai yi karya ba.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.