Yan Sanda 140 Sun Mutu Saboda Hawan Jini, an Gano Sauran Dalilan Mutuwarsu
- Hukumar 'yan sanda a Abuja ta bayyana yadda ya rasa jami'anta guda 140 a shekarar 2024 da ta wuce
- Hukumar ta ce an rasa jami'an ne saboda ciwon hawan jini da ayyukan ta'addanci da suka addabi birnin Abuja
- An tabbatar da cewa wasu jami'ai sun rasu a barci, yayin da wasu suka fadi suka mutu a wuraren aiki
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
FCT , Abuja - Rundunar 'yan sanda a Abuja ta bayyana cewa ta rasa jami'ai 140 a shekarar 2024 saboda hawan jini da ayyukan ta'addanci.
Rundunar ta ce wasu daga jami'an sun mutu ne suna tsaka da barci yayin da wasu suka mutu a bakin aiki.
Yadda wasu yan sanda suka mutu a Abuja
Kwamishinan yan sanda a birnin, Olatunji Disu shi ya tabbatar da haka a rahoton karshen shekara, cewar The Nation.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kwamishinan ya nuna takaici yadda rundunar ta rasa jami'anta da dama kuma masu kwazo a bakin aiki.
“Wasu daga cikin jami'an sun mutu a barci, yayin da wasu suka fadi suka mutu yayin da suke aiki.”
“Babban Birnin Tarayya na tsakiyar Najeriya, tana da iyaka da jihohin Neja, Kaduna, Kogi, da Nasarawa, tana matsayin cibiyar siyasa da kasuwanci."
"Matsayinta na musamman yana jawo hankalin mutane daban-daban, wasu da niyya mai kyau da wasu da mugun nufi.”
- Olatunji Disu
Haka kuma, ya bayyana cewa wasu daga cikin iyalan mamatan sun samu hakkokinsu da goyon bayan hukuma, Punch ta ruwaito.
Nasarar rundunar yan sanda a Abuja
"An samu rahoton laifuka 1,426, an kama mutane 1,077, kuma an kama mutane 71 a cikin mutane 263 da suka aikata fashi na 'one-chance’."
- Olatunji Disu
A game da shekara ta 2025, ya bayyana cewa za su kara mayar da hankali kan dabarun 'yan sanda na al'umma, aikin leken asiri, da wayar da kai ga jama'a.
Wani ya harbi abokinsa a otal din Abuja
Kun ji cewa yan sanda sun kama wani mutumi da ya buɗewa abokinsa wuta kan wata gardama da ta shiga tsakaninsu a ɗakin otal a Abuja.
Kwamishinam rundunar ƴan sanda, CP Olatunji Rilwan Disu ya ce jami'ai sun kwato mugayen makamai daga gidan wanda ake zargi.
Asali: Legit.ng