NNPCL Ya Fara Gyaran Matatar Kaduna, Za a Fara Aikin Tace Mai a Arewacin Najeriya

NNPCL Ya Fara Gyaran Matatar Kaduna, Za a Fara Aikin Tace Mai a Arewacin Najeriya

  • Kamfanin mai na kasa (NNPCL) ta tabbatar da cewa an fara aikin gyaran matatar mai ta Kaduna kamar na Warri da Fatakwal
  • NNPCL, karkashin Mele Kyari ta kashe akalla $2bn wajen farfado da matatun biyu, bayan shafe shekaru ana sa ranar da za su fara aiki
  • A martanin da kamfanin ya yi ga tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo, NNPCL ya ce yanzu gyaran matatar Kaduna ne a gaba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kaduna - Kamfanin mai na kasa (NNPCL) ya bayyana shirinsa na farfado da matatar Kaduna, watanni da gyara matatun Fatakwal da Warri.

Babban jami’in hulɗa da jama’a na NNPCL, Olufemi Soneye ne ya bayyana haka a cikin wata sanarwa da ya fitar a matsayin martani ga Olusegun Obasanjo.

Kara karanta wannan

"Ba karya muke ba," NNPCL ya gayyaci Obasanjo matatun da aka gyara a kan $2bn

NNPC Limited
NNPCL za ta fara gyaran matatar Kaduna Hoto: NNPC Limited
Asali: Facebook

Jaridar Premium Times ta wallafa cewa tsohon shugaban kasa, Obasanjo ya bayyana shakku a cikin kalaman NNPCL da gwamnatin tarayya na gyara matatu biyu a kasar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

NNPCL zai inganta matatun man Najeriya

Jaridar PrimeTimes ta wallafa cewa Kamfanin NNPCL ya ce yanzu haka matatar Fatakwal ta na iya tace mai ganga 150,000 a kowace rana.

Kamafnin ya bayyana cewa ita ma matatar Kaduna ta na kan hanya domin fara tace man fetur yadda dokokin duniya su ka tsara da tace mai.

NNPCL ta samu nasarorin farfado da matatu

Babban jami’in hulda da jama’a na NNPCL, Olufemi Soneye, ya ce shugaban kamfanin, Mele Kyari da hadin gwiwar shugaban kasa, Bola Tinubu sun yi kokari a fannin matatun fetur a kasar.

Soneye ya ce ɗaya daga cikin manyan nasarorin kamfanin shi ne gyaran matatun mai na Fatakwal da Warri, yayin da ake ci gaba da ƙoƙarin gyaran matatar mai ta biyu a Fatakwal da ta Kaduna.

Kara karanta wannan

PDP, Obi sun ba Tinubu lakanin samo waraka daga matsalolin Najeriya

Kamfanin NNPCL ta yi martani ga Obasanjo

A baya, mun wallafa cewa Kamfanin mai na kasa (NNPCL) ya tabbatar wa tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo da sauran 'yan Najeriya cewa matatun Fatakwal da Warri su na aiki.

Babban jami'in hulda da jama'a na kamfanin, Olufemi Soneye ne ya bayyana haka, inda ya ce babu shakku ko tantama a gyaran da NNPCL ya ce ya yi domin farfado da matatun Najeriya.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.