"An Shiga Wahala bayan Zaben Tinubu," Sanatan APC Ya Fadi Manufar Gwamnati
- Sanata Orji Uzor Kalu ya tabbatar da abin da 'yan Najeriya ke kuka a kai na matsin tattalin arziki da kuma tsadar rayuwa
- Kalu, wanda ke wakiltar Abia ta Arewa a Majalisar dattawan kasar nan ya ce abubuwa sun kara tabarbarewa a mulkin nan
- Amma ya mika fatansa na sabuwar shekara, tare da bayyana wa 'yan Najeriya manufar gwamnati a cikin sauran wa'adinta
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Abia - Sanatan da ke wakiltar Mazabar Abia ta Arewa, Orji Uzor Kalu, ya tabbatar da cewa wahalar da ‘yan kasar nan ke ciki ya karu tun bayan hawan mulkin Bola Tinubu.
Sanatan ya bayyana cewa gwamnati na sane da yadda aka samu karuwar matsi tun bayan da Bola Tinubu ya karbi mulki a watan Mayu na shekarar 2023.
Jaridar Daily Trust ta wallafa cewa amma Sanatan ya kara da tabbacin cewa Shugaban Kasa Bola Tinubu ya dauki wasu matakan da za su kawo karshen yunwa a nan gaba kadan.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sanata Orji Kalu ya kwantar wa jama’a rai
Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya na bakin kokarinsa domin ganin an fita daga halin matsi da jama’a suka shiga a gwamnatinsa.
Kalu, ya bayyana hakan yayin tattaunawa da manema labarai a yayin ziyarar sabuwar shekara da ya kai wa shugaban jam’iyyar APC na Jihar Ebonyi, Cif Stanley Okoro Emegha.
Sanatan Abia ya fadi kokarin Bola Tinubu
Sanata Orji Kalu ya jinjina da yadda shugaban Najeriya, Tinubu ya yi namijin kokari wajen sanar da jama’a cewa tabbas, an samu matsalar tattalin arziki.
Ya kara da cewa:
“Najeriya kasa ce da ke fama da matsanancin wahala tun bayan zuwan gwamnatin Shugaba Tinubu, amma idan ana tambayar ko akwai fata ga ‘yan Najeriya yanzu da muka shiga sabuwar shekara, bari in fada maku gaskiya, Shugaban Kasa Tinubu na aiki tukuru don rage wannan yunwar.
“‘Yan Najeriya suna jin yunwa, na san suna jin yunwa, amma yana aiki tukuru domin matakin da Shugaban Kasa ya dauka shi ne na bunkasa tattalin arziki.”
Sanata na hararar kujerar Tinubu
A wani labarin, kun ji cewa Sanatan APC da ke wakiltar Abia ta Arewa, Orji Uzor Kalu ya bayyana sha'awar tsaya wa jam'iyyarsa takarar shugaban kasa a zaben 2027.
Sanata Kalu, wanda tsohon gwamnan jihar Abia ne ya bayyana cewa ya na da gogewar siyasa da zai nemi kujerar, matukar shugaban kasa, Bola Tinubu ba zai sake nema ba.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng