Daga Zuwa Sasanta Rikicin Miji da Mata, An Kashe Wani Malamin Addini a Najeriya
- Wani malamin addini, Bishop Shina Olaribigbe ya rasa ransa yayin da yake kokarin sasanta wata rigima tsakanin wasu ma’aurata
- An ce mijin ya fusata bayan ya tarar da malamin a gidan matar, inda ya kai masa hari da wuka har ya halaka shi nan take
- Ma’auratan biyu sun shiga hannun ‘yan sanda yayin da bincike ke ci gaba da gudana domin gano gaskiyar abubuwan da suka faru
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Osun - An shiga fargaba a jihar Osun a safiyar Alhamis yayin da aka dabawa shugaban Cocin Rapture Empowerment International da ke Osogbo wuka har lahira.
Rahotanni sun bayyana cewa an kashe Bishop Shina yayin da yake kokarin sasanta wani rikici da ya ki ci ya ki cinyewa tsakanin wasu ma'aurata.
Malamin addini ya je sansata ma'aurata
Ba a bayyana sunan ma’auratan ba, amma an ce matar tana aiki a cocin Olaribigbe da ke unguwar BCGA a Osogbo, kamar yadda jaridar Punch ta rahoto.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Duk da cewa ba a raba aurensu a kotu ba, an ce ma’auratan sun sha samun sabani, wanda hakan ya sa suka daina zama a gida.
An ce mijin ya iso gidan matar ne da sanyin safiyar Alhamis kuma ya tarar da malamin cocin a cikin dakin matar.
Magidanci ya kashe malami a Imo
Ganin malamin cocin a cikin dakin matarsa ya fusata mijin sosai, wanda har ta kai shi ga kai masa hari da wuka, kamar yadda wata majiya daga coci ta shaida.
Majiyar ta kara da cewa:
"Sun samu cacar baki mai zafi, inda a karshe mijin ya dauki wuka ya soka wa malamin a kirjinsa. Ya mutu nan take."
Rahoton The Sun ta rahoto cewa bayan aukuwar lamarin, an kama ma’auratan biyu tare da kai su ofishin ‘yan sanda na Dugbe da ke Osogbo.
'Yan sanda sun tabbatar da kisan
A halin yanzu, an kai gawar Bishop Olaribigbe asibitin koyarwa na jami’ar Osun da ke Osogbo domin ci gaba da bincike.
Mai magana da yawun ‘yan sanda a jihar Osun, Yemisi Opalola, ta tabbatar da faruwar lamarin a wata sanarwa.
"An ce mijin ya yi zargin cewa malamin yana da wata alaka ta soyayya da matarsa, wanda hakan ya sa ya aikata wannan mummunan abu."
- A cewar Yemisi Opalola.
Malamin addini ya kashe yaro a Imo
A wani wani labarin, mun ruwaito cewa wani limamin cocib Katolika a jihar Imo ya kashe wani yaro ta hanyar harbinsa da bindiga a cikin harabar cocin.
Rundunar 'yan sanda ta cafke limamin wanda aka ce ya kashe yaron saboda yaron ya kunna bama baman wasa a harabar cocin lokacin murnar sabuwar shekara.
Asali: Legit.ng