An Shiga Tashin Hankali: Malamin Addini Ya Sa Bindiga Ya Harbe Wani Yaro har Lahira
- Wani malamin Katolika ya harbi wani yaro a cocin St. Colombus yayin da yaron ya kunna bama-baman wasa a harabar coci
- Rundunar 'yan sanda ta tabbatar da kama malamin yayin da bincike ke ci gaba don gano hakikanin dalilan da ya janyo harbin
- Kwamishinan 'yan sanda ya jaddada dokar hana amfani da bama-baman wasa a Imo a lokutan bukukuwan sabuwar shekara
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Imo - Wani malamin Katolika a Najeriya ya sa bindiga ya harbe wani yaro har lahira bayan yaron ya kunna bama-baman wasa a cikin harabar coci.
Rahotanni sun bayyana cewa lamarin ya faru ne yayin taron bauta na Crossover domin shiga sabuwar shekara ta 2025.
Malamin addini ya harbe yaro har lahira
Jaridar Premium Times ta rahoto cewa taron bautar ya gudana ne a Cocin St. Colombus Parish Amaimo, da ke karamar hukumar Ikeduru, jihar Imo.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sai dai ba a tabbatar da sunan malamin Katolikan ko na yaron da aka kashe ba yayin da aka rubuta wannan rahoto.
Henry Okoye, mai magana da yawun 'yan sandan jihar Imo, ya tabbatar da faruwar lamarin cikin wata sanarwa a ranar Alhamis.
'Yan sanda sun cafke malamin addinin
Kakakin 'yan sanda ya shaida cewa:
“Mun fara cikakken bincike domin gano hakikanin abubuwan da suka jawo lamarin,”
- Inji Okoye, jami’in dan sanda mai mukamin ASP
Henry Okoye ya tabbatar wa manema labarai cewa an kama malamin Katolikan da ake zargi da hannu cikin lamarin.
“Yana hannunmu yanzu,” a cewar Mista Okeye, yana nuni da malamin Katolikan da aka tsare.
'Yan sanda na binciken lamarin
Da aka tambayi mai magana da yawun 'yan sandan game da yanayin da lamarin ya faru da kuma yadda malamin ya sami bindigar sai cewa ya yi:
“Ba zan iya cewa ya yi hakan da gangan ba. Amma muna ci gaba da bincike."
Rundunar 'yan sanda ta Najeriya ta haramta amfani da bama-baman wasa da ake kunnawa yayin bukukuwan Kirsimeti da na sabuwar shekara.
An hana kunna bama-baman wasa
Kwamishinan 'yan sanda na jihar Imo, Aboki Danjuma, ya kara jaddada dokar hana sayarwa da amfani da bama-baman wasa a ranar 1 ga Disamba 2024.
Wannan matakin na hukuma na nufin rage matsalolin tsaro da aka saba fuskanta yayin bukukuwan sabuwar Shekara a jihar.
An kama malamin musulunci a Zamfara
A wani labarin, mun ruwaito cewa kungiyar 'yan banga a jihar Zamfara sun cafke wani malamin addinin Musulunci bisa zargin taimakawa 'yan bindiga.
A lokacin da ake yi wa malamin tambayoyi a bidiyo, ya amsa laifinsa tare da bayyana cewa yana yi wa 'yan bindigar 'addu'ar neman sa'a' idan sun fita kai hari.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng