Duk da Rasa Kujerarsa, Tsohon Minista a Kano Ya Koda Tinubu, Ya Yabi Yan Najeriya
- Tsohon Ministan Gidaje, Dr. Abdullahi Tijjani Gwarzo, ya yaba wa Bola Tinubu kan jagoranci da gyare-gyare don ci gaban Najeriya
- Gwarzo ya jinjina wa 'yan Najeriya bisa jajircewa wajen tallafa wa hangen nesa na Shugaba Tinubu
- A sakon sabuwar shekara, Gwarzo ya ce yana sa ran ci gaba da samun zaman lafiya da wadata a shekarar 2025
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
FCT, Abuja - Tsohon Ministan gidaje da raya birane, Dr. Abdullahi Tijjani Gwarzo, ya yaba wa salon mulkin Shugaba Bola Tinubu.
T. Gwarzo ya yaba wa shugaban ne kan jajircewarsa wajen sake gina Najeriya ta kowane bangare.
Tsohon Minista ya yabawa mulkin Tinubu
Hakan na kunshe ne a sakon sabuwar shekara, wanda ya wallafa a wata sanarwa da ya sanya wa hannu, cewar Leadership.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwarzo ya kuma yaba wa 'yan Najeriya kan sadaukarwa da goyon baya ga manufofin shugaban.
"Na mika gaisuwar sabuwar shekara ga mai girma shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu GCFR."
"A yayin shiga sabuwar shekara, ni, Abdullahi Tijjani Gwarzo FTRAN, tsohon Ministan gidaje da raya birane na mika gaisuwata ga Shugaban Kasa."
"A cikin wannan sabuwar shekara, ina jinjina wa shugaban bisa jagorancin da ya yi tare da daukar matakan da suka dace wajen farfado da Najeriya ta kowane fanni."
"Daga sauye-sauyen tattalin arziki zuwa matakan magance matsalolin tsaro, na yi matukar gamsuwa da karfin hali da jajircewar da ya jagoranci kasarmu mai girma."
- Abdullahi Gwarzo
Tsohon Ministan ya yi wa Tinubu fatan alheri
Gwarzo ya kuma bayyana kwarin gwiwa cewa jajircewar shugaba Tinubu zai kawo mafita ga matsalolin kasar, musamman a fannin tsaro da farfado da tattalin arziki.
"Ina fatan ganin Najeriya ta cigaba a shekarar 2025, yayin da muke hada kai wajen gina kasa mai albarka."
"Ina yi wa shugaban Tinubu fatan karin karfi, hikima, da lafiya a sabuwar shekara."
- Cewar tsohon Ministan
Gwarzo: Tsohon Minista ya magantu bayan tsige shi
Kun ji cewa tsohon Minista, Abdullahi T. Gwarzo ya bayyana cewa Bola Tinubu ya sauke shi daga muƙamin minista ne saboda ya naɗa ɗan Kano ta Tsakiya.
Gwarzo ya ce Nasiru Gawuna ya kamata a fara yi wa tayin kujerar kafin a ɗauko wani inda ya ce ba shi da wata matsala da wanda aka ba mukamin.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng