"Ba za Mu Saurarawa Gwamnati ba," ASUU Ta Fadi Abin da ke Kashe Ilimi a Najeriya
- Kungiyar malaman jami'o'i ta kasa (ASUU) ta bayyana damuwa bisa ci gaba da tabarbarewar ilimi a Najeriya
- Shugaban kungiyar reshen jami'ar Ibadan, Farfesa Ayo Akinwole ne ya bayyana damuwarsu a sakon sabuwar shekara
- Ya ce kwararrun malamai yanzu na gudun koyarwa a makarantun gwamnati, yayin da kudin masu zaman kansu ya gagari jama'a
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Oyo - Kungiyar malaman jami’o’i ta kasa (ASUU) ta bayyana damuwa a kan yadda gwamnati ke tafiyar da ilimi da malaman jami’o’in gwamnati.
Kungiyar ASUU ta ce wannan babban sakaci ne da ke hana ƙwararrun malamai sha’awar shiga aikin koyarwa, wanda hakan ke lalata tsarin ilimi.
Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa Farfesa Ayo Akinwole, Shugaban ASUU na reshen jami’ar Ibadan, ya ne bayyana damuwarsu a cikin saƙon sabuwar shekara.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
'Yan ASUU sun fadi kalubalen ilimi a Najeriya
Tashar Arise TV ta ruwaito cewa ASUU ta nuna damuwa kan yadda ba malamai na jami’o’i kawai ba, har da na firamare da sakandare ke fama da ƙarancin albashi.
Kungiyar ta ce wannan matsala ta haifar da ƙwararrun malamai, lamarin da ya sanya kafa makarantu masu zaman kansu, waɗanda mafi yawan iyalai ba sa iya biyan saboda tsada.
ASUU ta nemi a inganta jin daɗin malamai
Farfesa Akinwole ya jaddada cewa kasafin kuɗin Najeriya na ilimi a shekarar 2025, wanda ya ware 7% daga jimlar kasafin kuɗin, ya gaza ƙa’idar 15%-20% da UNESCO da UNFPA suka ba da shawara.
Ya yi kira ga gwamnatin Bola Tinubu da ta sake dubawa da rattaba hannu kan yarjejeniyar da aka tattauna kuma aka cimma a baya.
Ya ce matukar gwamnati ta ci gaba da biris da bukatunsu, kungiyar ASUU za ta mayar da kakkausan martani domin a samu inganta ilimi.
Kungiyar ASUU za ta fara yajin aiki
A baya, kun ji cewa kungiyar malaman jami'o'i ta kasa (ASUU) ta yi barazanar tsunduma yajin aiki, matukar gwamnatin tarayya ta ci gaba da jan kafa a wajen biyan bukatunta.
Shugaban ASUU na kasa, Farfesa Emmanuel Osodoke ne ya bayyana haka, ya ce sun dade suna ba gwamnati damar ta duba yarjejeniyar da su ka cimma a shekarun baya.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng