Gwamnatin Legas ta ce a koma karatu, ‘Yan ASUU da SSANU sun rufe kofar LASU

Gwamnatin Legas ta ce a koma karatu, ‘Yan ASUU da SSANU sun rufe kofar LASU

- A yau Gwamnatin Legas ta ce a bude Jami’o’i domin a cigaba da karatu

- ‘Yan kungiyoyin ASUU, NASU, da SSANU su na zanga-zanga a LASU

- Wannan ya sa aka hana kowa shiga cikin harabar jami’ar ta Legas dazu

Labari ya na zuwa mana yanzu cewa an gagara shiga jami’ar jihar Legas watau LASU, duk da cewa gwamnati ta bada umarnin cewa a koma aiki a yau.

A ranar 14 ga watan Satumba, 2020 ne aka tsara cewa za a koma karatu a jami’ar ta Legas. Wannan yunkuri ya gamu da cikas daga ma’aikatan da ke yajin-aiki.

Jaridar The Cable ta ce ‘yan kungiyar ASUU ta malaman jami’a da SSANU na manyan ma’aikatan jami’ar sun hana kowa shiga cikin harabar jami’ar LASU.

KU KARANTA: An rufe makarantu bayan COVID-19 ta sake dawowa a Faransa

Sauran wadanda su ka rufe makarantar su na zanga-zanga sun hada da ‘yan kungiyar NASU da NAAT.

Rahotanni sun ce daga cikin wadanda su ka gagara shiga cikin makaranta a safiyar yau har da shugaban jami’ar ta jihar Legas, Olanrewaju Fagboun SAN.

Jagororin kungiyoyin SSANU, ASUU, NASU da NAAT sun hana kowa shiga jami’a domin a koma aiki. Wasu daga cikin wadannan ma’aikata su na yajin aiki.

Tun farkon shekarar nan malaman makarantun jami’a su ke faman yajin aiki, a sakamakon tursasa masu da gwamnati ta yi na komawa tsarin biyan albashi na IPPIS.

Gwamnatin Legas ta ce a koma karatu, ‘Yan ASUU da SSANU sun rufe kofar LASU
Jami'ar LASU Hoto: Facebook/lagosstateuniversityadmission
Asali: Facebook

KU KARANTA: Gwamnati ta yi amai, ta lashe game da shirin bude Makarantu

Bayan tafiyar ASUU yajin-aiki, sauran takwarorinsu sun yi barazanar su ma za su shiga yajin, sun koka da cewa ana zaftare masu albashi tun da su ka shiga IPPIS.

Ita dai gwamnatin jihar Legas ta bukaci daliban da ke ajin karshe a jami’a su koma makaranta domin su samu damar karkare zagon karatun da ya rage masu.

Gwamnati ta rufe makarantu a Najeriya ne sakamakon annobar COVID-19. Hukumomin kasar su na gudun a samu barkewar cutar COVID-19 wajen daukar karatu.

Kwanaki kun ji Ministan ilmi ya ce ba su gamsu da kiran a sake bude makarantu ba.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng