Sanatan Kaduna Ya Sha da Kyar, An Nemi Raba Shi da Rayuwarsa, Ya Fadi Yadda Aka Yi
- Wasu yan daba sun kai wani hari domin neman rayuwar Sanata Lawal Adamu Usman a jihar Kaduna
- Sanata Lawal Usman da ke wakiltar Kaduna ta Tsakiya a Majalisar Dattawa ya sha da kyar yayin harin
- Sai dai sanatan bai ba da cikakken bayani kan lamarin ba yayin da yake zargin ana neman raba shi da rayuwarsa
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Kaduna - Sanata Lawal Adamu Usman daga jihar Kaduna ya tsallake rijiya da baya a farkon shekarar nan.
Sanatan da ke wakiltar yankin Kaduna ta Tsakiya ya ce an yi yunkurin hallaka shi kafin Allah ya tseratar da shi.
An yi yunkurin yi wa Sanata kiranye
Sanata Lawal ya bayyana haka ne a shafinsa na Facebook a jiya Laraba 1 ga watan Janairun 2024.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sanata Lawal a baya ya ci karo da matsala da wata kungiya ta bukaci yin kiranye ga sanatan da ke wakiltar Kaduna ta Tsakiya.
Sai dai Sanatan ya caccaki kungiyar da ta yi wannan kira inda ya ce ba zai bata lokacinsa wurin fahimtar da su irin ayyukan da yake yi ba.
Hakan ya biyo bayan kiranye da kungiyar Kaduna Peace and Tranquility Forum (KPTF) ta yi ga sanatan saboda zargin rashin iya wakilci nagari.
Sanatan Kaduna ya tsallake rijiya da baya
A cikin sanarwar da ya wallafa, Sanata Lawal bai ba da cikakken bayani ba kan lamarin wanda ta jawo martanin mutane da dama.
Iyakarta dai ya ce abin ya faru ne a yankin Kaduna ta Arewa, daya daga cikin mazabun da yake wakilta a majalisarr dattawan Najeriya.
"Yanzun nan na kubuta daga wani hari na neman raba ni da rayuwata da wasu miyagu suka yi a mazabar Kaduna ta Arewa."
- Sanata Lawal Adamu Usman
Har zuwa lokacin tattara wannan rahoto ba mu ji wata sanarwa daga hukumomi kan wannan lamari ba.
Sanata Shehu Sani ya ba yan Arewa shawara
Kun ji cewa Shehu Sani ya bayyana cewa kamata ya yi Arewa ta hakura ta bar yan Kudu su ci gaba da mulkin Najeriya a babban zaɓen 2027.
Tsohon sanatan Kaduna ta tsakiya ya ce daga nan kuma Arewa za ta samu cikakkiyar damar samar da shugaban ƙasa a shekarar 2031.
Ya kara da cewa Bola Tinubu ya cancanci ya kara samun goyon bayan yan Arewa saboda abin da ya yi masu lokacin zaben 2015.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng