Abin da Tinubu Ya Fadawa Gwamnonin Najeriya a Lagos, Ya ba Su Shawara
- Shugaba Bola Tinubu ya tabbatar da muhimmancin haɗin kai tare da gwamnoni, ya ƙaryata rahotannin rashin jituwa kan ƙananan hukumomi
- Tinubu ya bukaci gwamnoni su mai da hankali kan ci gaban al’umma, yana tabbatar musu babu niyya ta karɓar ikon ƙananan hukumomi
- Shugaban ya yabawa kokarin gwamnoni, yana kira da a yi aiki tare don magance matsalolin ƙasa da haɓaka tattalin arziki
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
FCT, Abuja - Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya mayar da martani kan zargin alakarsa da gwamnonin Najeriya ta yi tsami.
Tinubu ya jaddada muhimmancin haɗin kai da gwamnoni, ya ƙaryata rahotannin rashin jituwa kan harkar mulkin ƙananan hukumomi.
Bola Tinubu ya nemi hadin kan gwamnoni
Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da hadiminsa, Bayo Onanuga ya wallafa a shafin X.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Tinubu ya fadi haka ne yayin ziyarar sabuwar shekara da mataimakinsa, Kashim Shettima da Gwamnonin Najeriya suka kai masa a gidansa da ke Lagos.
Shugaban ya ce haɗin kai ne kawai zai taimaka wajen kawo ci gaba a fadin Najeriya baki daya.
Ya bayyana cewa haɗin kai na da matuƙar muhimmanci wajen kawo ci gaba ga matakin ƙananan hukumomi.
Shugaba Tinubu ya fadi alakarsa da gwamnoni
“Ba za mu yi fada ba, ku kula da ƙananan hukumomin ku, ku tabbatar kun cika burin al’umma a matakin ƙasa."
“Ku ne muhimmiyar alaƙar da ke haɗa Najeriya da ci gaba, ku ne masu mallakar ƙasa, kuma aikin yana hannunku."
- Bola Tinubu
Tinubu daga bisani, ya kuma ƙara da cewa babu rashin jituwa game da ikon ƙananan hukumomi.
Abba Kabir ya tura bukata ga Tinubu
Kun ji cewa Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf tare da takwarorinsa sun ziyarci shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu a gidansa.
Gwamnonin sun kai ziyarar a ranar 1 ga watan Janairu, 2025 ne domin taya shugaba Tinubu murnar shiga sabuwar shekara.
Gwamna Abba Kabir ya yi amfani da damar wajen tunatar da Tinubu muhimmancin kara habaka tattalin arzikin Kano.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng